Shugabar Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP, Zainab Nda-Isaiah, ta bayyana damuwarta kan yadda ƴan jarida da marubuta ke shiga cikin matsin tattalin arziki, duk kuwa da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen fito da ra’ayin jama’a da kawo sauyi a cikin al’umma.
Da take jawabi a wajen taron baje kolin littafin ‘Writing for Media and Monetising it’ na Azubuike Ishiekwene, ta jaddada rashin jin daɗin halin da marubuta da yawa suke ciki, musamman na talauci. Ta yi imanin cewa littafin Ishiekwene zai zamo tamkar jagora wajen taimakawa marubuta su gane hanyar tudun dafawa da kuma samun kuɗi.
- NLC Ta Bukaci A Kara Wa ‘Yan Jarida Albashi, Inshora Da Fansho
- Minista Ya Kaddamar Da Taron Horas Da ‘Yan Jarida Kan Yaƙi Da Aƙidun Ta’addanci
Zainab ta bayyana littafin a matsayin cikakken jagora wanda ba kawai ya shafi tsarin rubuce-rubuce ba, har ma da jan hankali kan amfani da fasahar rubuce-rubuce wajen dogaro da kai.
Ta kuma yaba wa Ishiekwene babban edita kuma babban mataimakin shugaban rukunin kamfanin LEADERSHIP bisa jajircewarsa da sanin ya kamata, wanda hakan ya taimaka matuka wajen ci gaban littafin.
Taron wanda ministan yada labarai da wayar da kan jama’a Mohammed Idris ya jagoranta, ya samu halartar manyan mutane irin su Sanata Ireti Heebah Kingibe, da mawallafin jaridaer Vanguard Sam Amuka, da Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo, SAN, da tsohon kakakin shugaban kasa Dr. Reuben Abati, fitaccen marubucin jarida kuma mai gabatar da shirye-shiryen talabijin.