Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da dakatar da gudanar da zabe a wasu wurare a jihar Kogi, sakamakon wasu rahotanni da aka samu na magudin zabe.
An tafka kura-kurai a lokacin zaben, ta hanyar rubuta sakamakon zaben kafin kammala kada kuri’a a kananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi, da Okene.
- Allah Ya Yi Wa Fitaccen Tsohon Dan Wasan Hausa, Usman Baba (Samanja) Rasuwa
- Hanyoyin Tsaftace Jiki Bayan Saduwa
Sai dai lamarin ya fi kamari a yankin Ogori/Magongo.
Hukumar ta yi kakkausar suka ga wadannan abubuwan da suka faru, inda ta bayyana cewa ba za ta amince da lamarin ba.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu ya jaddada cewa duk wani sakamakon da bai samo asali ba daga tsarin da hukumar ta kafa a rumfunan zabe ba za ta amince da shi ba.
Wannan lamari ya sanya dakatar da zaben a Unguwa Tara a karamar hukumar Ogori/Magongo—musamman Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi, Ugugu, Obinoyin, Obatgben, da Oturu—a halin yanzu.
Ana ci gaba da gudanar da bincike a wasu kananan hukumomin, kuma za a ci gaba da tattara sakamakon zaben.
A yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, hukumar na bin diddigin ma’aikata da kayan aiki don gano wadanda suka taka rawa wajen tafka magudi a jihar.
INEC ta tabbatar wa masu kada kuri’a a jihar Kogi cewa za a kare kuri’unsu, kuma za a mutunta zabin dimokradiyya.
Hukumar tun a baya ta jadadda kudirinta wajen tabbatar da sahihin zabe.