Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa an cire sunayen matattun masu kada kuri’a har guda 7,746 daga rajistar masu zabe a jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja a zuwa watan Disambar 2022.
Daraktar wayar da kan jama’a da masu kada kuri’a, Bictoria Etta-Messi ce ta bayyana hakan ga manema labarai.
- A Shirye Kasar Sin Take Ta Kyautata Dangantakar Tattalin Arziki Da Amurka
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
“Mutane dubu bakwai da dari bakwai da arba’in da shida sun ragu a fadin jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja daga rajistar masu kada kuri’a zuwa watan Disamba 2022,” in ji ta.
A cewar hukumar INEC, ana tsaftace rajistar masu kada kuri’a kafin kowane babban zabe.
A bitar zaben 2023 bayan kammala zabe a watan Disamba na 2024, INEC ta bayyana kalubalen da ke tattare da tsaftace rajistar masu kada kuri’a, duk da ingantuwar tsarin rajistar masu kada kuri’a da aka samu wanda ya kara sabbin masu rajista har guda 12,298,944.
Wani babban batu shi ne, wahalar cire wadanda suka mutu sakamakon gibin bayanan mutuwar a hukumance.
“Matsalolin da ke tattare da bayanan mutuwar jami’ai na ci gaba da yin wahala ga INEC wajen cire wadanda suka mutu rajistar zabe,” in ji hukumar.
Hukumar ta kuma gano matsalar yin rajista sau biyu ko kuma da yawa, wanda aka magance ta hanyar tura na’urar tantance bayanan masu kada kuri’a.
Wannan tsari ya ba da alama tare da cire shari’o’in 2,780,756 na rajista marasa inganci, wanda ke wakiltar kashi 22.6 na duk sabbin masu rajista a fadin kasar nan.
INEC ta kara nuna damuwa game da raguwar fitowar masu kada kuri’a. Zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar a shekarar 2023, ya samu fitowar kashi 27.5 cikin 100, inda ya ragu da kashi 35.6 a shekarar 2019.
Wasu masu ruwa da tsaki sun alakanta wannan raguwar wani bangare na hauhawar rajistar masu kada kuri’a tare da yin kira da a kara himma wajen tsaftace ta.
Masu ruwa da tsaki a wannan bitar sun ba da shawarar cewa ya kamata INEC ta karfafa hadin gwiwa da hukumomi irinsu hukumar kula da yawan jama’a ta kasa (NPC) da kuma hukumar kula da tantance ‘yan kasa (NIMC) domin tantance wadanda suka mutu.
Akwai kuma kiraye-kirayen a dakatar da mutanen da ba su yi zabe ba a zabuka uku da suka gabata da kuma bukatar su sake sabunta rajistarsu.
“Shawara daya daga cikin wannan bita ita ce a karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomi irinsu NIMC da NPC don zakulo wadanda suka rasu a cikin rajista da cire su. Bugu da kari, hukumar za ta iya dakatar da mutanen da ba su yi zabe ba a zabuka uku da suka gabata daga rajistar tare da neman su sabunta rajistarsu,” in ji INEC a bitarta.