Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), ta mayar wa da fitaccen mawakin nan Davido, martani kan furucinsa a kan rashin mika wa sabon zababben gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, takardar shaidar lashe zaben gwamnan jihar.
INEC a cikin sanarwar da kwamishinanta kuma shugaban kwamitin ilimantar wa da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya fitar ta ce, “Bisa doka ba a ce lallai sai an mika wa Adeleke takardar shaidar lashe zaben a cikin awanni 24 ba kamar yadda Davido ya yi ikirarin ba.
- NEMA Ta Raba Tallafi Ga ‘Yan Hijira 24,000 A Katsina
- An Sace Shugaban Jam’iyyar APC Na Edo, ‘Yan Sanda Sun Baza Koma
Davido ya yi ikirarin nasa ne a Twitter, inda ya kalubalanci INEC kan kin mika wa Adeleke takardar shaidar lashe zaben a cikin awanni 24.
Okoye, ya ce, kwanaki 14 ne suka rage a mika wa Adeleke takardar shaidar lashe zaben, inda ya sanar da cewa, INEC ba jam’iyyar siyasa ba ce kuma ba za ta sa kanta, a cikin harkar siyasa ba.
A cewarsa, sashe na 72 na dokar zabe da aka sabunta ya ba da umarnin a bai wa wanda ya lashe zabe takardar shaidar a cikin kwanaki 14.