Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta musanta zargin cewa jami’anta a jihar Adamawa sun ci amanar aikinsu bayan wata ziyarar sirri da suka kai gidan gwamnati da daddare.
A cikin wata sanarwa da kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a Festus Okoye ya fitar a ranar Alhamis, tace, INEC ta musanta dukkan zarge-zargen da ake yi mata, ta kuma nanata cewa, ba a gudanar da irin wannan taron ba kafin sake zaben da aka gudanar a ranar Asabar 15 ga Afrilu, 2023.
“Irin wannan taron, ya saba wa rantsuwar da muka yi na tsaya wa tsaka-tsaki.” Inji shi.
Okoye ya jaddada cewa hukumar ta nada jami’in da zai kawo mata sakamakon zaben gwamna daya tilo wanda kuma matsayinsa ya ninka matsayin jami’in tattara bayanan zaben shugaban kasa.
Kwamishinan INEC na kasa ya sake nanata cewa “Ba Mu Ware Adamawa Don Ta Zama Filin Daga Ba ” don haka ya bukaci jama’a da su “daina amfani da zargi mara tushe”.