Mista Festus Okoye, kwamishinan hukumar INEC na kasa mai kula da sashen wayar da kan masu kada kuri’a da watsa labarai, ya tabbatar da cewa hukumar ta shirya tsaf domin gudanar da zaben da ba a kammala ba a duk fadin jihar Kebbi.
Ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida jim kadan bayan raba muhimman kayyakin ga kananan hukumomin da karasa zaben ya shafa a hedikwatar INEC na jihar da ke Birnin Kebbi a ranar Juma’a.
Za a gudanar da zaben gwamnan da ba a kammala ba a rumfunan zabe 142 da ke fadin kananan hukumomi 20 daga cikin kananan hukumomi 21 na jihar.
Za a sake gudanar da zabuka a yankin Sanatan Kebbi ta Arewa, mazabar tarayya biyu da kuma mazabun ‘yan majalisar dokoki na jihar gudu takwas.
Kwamishinan ya bayyana jin dadinsa cewa hukumar ta kammala rabon kayan zabe masu muhimmanci da suka hada da; takardun zabe, takardar sanya sakamakon zabe da na’urorin BVAS don tantance masu jefa kuri’a a rumfunan da abin ya shafa.
Ya ce, “Hukumar INEC na da hulda da masu ruwa da tsaki da jam’iyyun siyasa daban-daban, kungiyoyin farar hula da kuma kungiyoyi domin tabbatar da an gudanar da zabukan da ba a kammala ba yadda ya dace.”
Hakazalika Kwamishinan dai ya kara da cewa shugabannin hukumomin tsaro sun yi alkawarin cewa su na da jajircewa, iyawa da kuma kayan aiki don tabbatar da an gudanar da dukkan sauran zabuka da ba a kammala a cikin tsaro da kwanciyar hankalin a duk wuraren da abin ya shafa, “Ma’ana jami’an tsaro sun shirya tsaf bisa ga tabbacin da suka baiwa hukumar zabe,” inji mista Festus Okoye.
“A namu bangaren shugaban hukumar ya tura kwamishinonin kasa uku jihar Kebbi saboda yawan zabukan da muke da su a nan, ya kuma tura ma’aikatan da za su jagoranci wannan zabe na musamman.
“Don haka, za mu samu mafi yawan ma’aikatanmu da za su yi aiki a matsayin Shugabannin kula da sanya ido watau turawan zabe, LG Tech da kuma yin ayyuka daban-daban don tabbatar da cewa an gudanar da zabukan cikin nasara.
“Ba za mu sake yin wani karin zabe ba, za mu kammala zaben nan, don haka a ranar Lahadi ‘yan Kebbi za su iya sanin wanene Gwamnan su kamar kowace jihar ta tarayya,” in ji shi.