- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), ta bayyana samar da sashen ƙirƙirarriyar basira wato AI, a sashin yaɗa labarai da fasaha na hukumar.
Hukumar ta sanar da wannan matakin ne a taron da take yi na duk sati wanda ya wakana a yau Alhamis 22 ga watan mayun 2025 a cikin shirin da take yi na ƙarfafa AI domin bunƙasa harkokin zaɓe.
- Sanata Adamu Aliero Ya Ƙaddamar Da Rabon Kayan Tallafi Ga Ƙananan Hukumomi Takwas A Kebbi
- Kocin Super Eagle Ya Gayyaci Ahmed Musa Buga Gasar Kofin Unity A Landan
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma shugaban kwamitin sashen wayar da kan jama’a da ilimintar da su a harkokin zaɓe, an fito da wannan tsarin ne domin yadda AI ke ci gaba da faɗaɗa musamman a harkokin zaɓe a duniya.
“Hukumar ta amince da ƙirƙiro sashen AI a ƙarƙashin ɓangaren fasahar sadarwa na hukumar domin cin ribar AI da fasahar da take ɗauke da ita da kuma magance ɓarnar da fasahar ka iya kawowa a lokutan zaɓe” a cewar sanarwar
Wannan matakin da INEC ta ɗauka dai ya biyo bayan tarurruka da dama da ma’aikatan hukumar suka halarta a sassa daban-daban na duniya a kan AI inda ƙasashen Afirka da dama suka tattauna domin rungumar sabuwar basirar ta hanyar yin amfani da ita a inda ya dace da kuma maganin yin amfani da ita wajen kawo cikas a zaɓe musamman yaɗa labarun ƙarya a lokutan zaɓe da sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp