Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Ƙasa (INEC) ta tilasta wa daraktocinta hudu yin ritaya.
Shugaban Kwamitin Wayar da Kan Masu Jefa Ƙuri’a a hukumar, sannan Kwamishinan Tarayya, Mista Sam Olumekun, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
- ‘Yansanda Sun Kashe Wasu Da Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane 6, Sun Kwato Kudade A Bauchi
- Tinubu Ya Yi Allah-Wadai Da Harin ‘Yan Ta’adda A Filato
Umurnin yin ritayar ya biyo bayan fara aiki da sabuwar dokar da ta ƙayyade wa’adin shekaru takwas ga kowane daraktan da ke aiki ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya.
Olumekun ya ce, “Bisa aiki da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar a cikin wata sanarwa mai lamba HSCF/SPSO/268/T3/2/37, wadda aka fitar a ranar 27 ga Yuli, 2023, Hukumar Zaɓe ta bi wannan umarnin ta hanyar umartar dukkan daraktocin da su ka shafe shekaru takwas su na aiki a INEC, ko sama da haka, da su gaggauta yin ritaya.
“Bisa tsarin wannan umarni, daraktoci huɗu daga INEC za su ajiye aiki su tafi ritaya. Biyu daga cikinsu Shugabannin Sassa ne a Hedikwatar INEC da ke Abuja, sauran biyun kuma Sakatarorin Tsare-tsaren Ayyuka ne a wasu ofisoshin hukumar da ke jihohi.”
Sai dai kuma ya yi ƙarin hasken cewa, wannan tsarin bai shafi manyan jami’an hukumar masu aiki a ɓangaren kula da lafiya ba, kamar yadda ita kan ta takarda mai lamba MH 7205/T31 ta nuna, wadda aka fitar a ranar 7 ga Satumba, 2023.
“Hukumar Zaɓe na yi wa daraktocin da sallamar ta shafa fatan alheri a rayuwar da za su ci gaba, bayan yin ritayarsu,” inji Mista Olumekun.