Rundunar ‘yansanda a jihar Bauchi tare da hadin gwiwar kungiyoyin ‘yan sa-kai sun kashe wasu mutane 6 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi al’ummar Bauchi a karamar hukumar Ningi.
LEADERSHIP ta samu cewa, a yayin samamen, ‘yansandan sun kuma kwato Naira miliyan N4,580,000 daga maboyar barayin bayan an yi artabu da su.
- Saurayi Ya Kashe Budurwarsa A Kan 5000 A Bauchi
- An Masa Daurin Rai Da Rai Saboda Yin Fyade A Masallaci A Bauchi
Wadanda ake zargin sun kashe mutane sama da 8 da suka hada da sarakunan gargajiya biyu a yankin Kada da Gamiji da ke gundumar Burra, Ningi a watan Yulin bana.
Talla
Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Bauchi, Auwal Musa Mohammed, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Ningi ranar Laraba.
Talla