Yayin da saura kwanaki 66 a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dattawa, Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya tabbatar da cewa hukumar sa za ta yi amfani da motocin sufuri har 100,000 da kuma jiragen ruwa 4,200 domin raba ma’aikata da kuma kayan zaɓen 2023.
Yakubu ya bayyana haka a lokacin wani ƙwarya-ƙwaryan bukin sa hannu kan yarjejeniyar da INEC ta cimma tare da ƙungiyoyin motocin sufuri da na jiragen ruwa, ranar Talata a Abuja.
Ya ce INEC za ta yi amfani da su ne domin tabbatar da cewa karakainar raba kayan zaɓe da jami’an zaɓe bai samu wata tangarɗa kafin ranar zaɓe da kuma ranar zaɓen ba.
Shugabannin ƙungiyoyin sufurin da INEC ta ƙulla yarjejeniyar da su, uku ne da su ka haɗa da ƙungiyar direbobi ta NURTW, Kungiyar Masu Motocin Sufuri wato NARTO da kuma Ƙungiyar Mataikatan Jiragen Ruwa, MWUN.
“INEC za ta yi amfani da motoci 100,000, jiragen ruwa 4,200 da kuma ma’aikatan zaɓe miliyan ɗaya.
“Hakan ne ya sa mu ka ƙulla wannan yarjejeniya da ƙungiyoyin sufuri uku domin tabbatar da komai ya tafi daidai a cikin nasara, kamar yadda aka tsara.
“Waɗannan motoci da jiragen ruwa za su yi karakainar ɗaukar jami’an zaɓe da kayan zaɓe sau biyu kenan a lokacin zaɓen ranar 25 ga Fabrairu da kuma ranar 11 ga Maris, 2023. Za su yi aikin jirga-jirgar kai kayan zaɓe da jami’an zaɓe a dukkanin ƙananan hukumomi 774, mazaɓu 8,809 da kuma rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin ƙasar nan.
“Za a riƙa yi wa jiragen ruwan da ke ɗauke da kayan aiki kariya da samun rakiyar sojoji ɗauke da makamai a cikin ƙananan jiragen ruwa na yaƙi.”
Yakubu ya bada tabbacin cewa tun ƙarfe 8:30 na safiyar 25 ga Fabrairu, 2023 jami’an zaɓe za su fito domin fara tantance masu jefa ƙuri’a. Sannan kuma ya ce baya ga motoci da jiragen ruwa, INEC za ta yi amfani da Keke NAPEP da babura domin isar da kayan aikin zaɓe cikin kowane lungu.
Daga nan ya umarci shugabannin ƙungiyoyin motocin sufurin su sani cewa wannan yarjejeniyar da su ka sa hannu, tamkar rantsuwa ce cewa ba za su aikata ba daidai ba.
Ya ce su ja kunnen direbobin su kada su nuna son kai ko fifita wani ɗan takara ko wata jam’iyya. Kuma kada su haɗa kai da jami’an tsaron da za a riƙa haɗa su aikin kariya da tsaro su yi amfani da kayan zaɓe ta hanyar da ba ta dace ba.
Shugaban NURTW, Tajuddeen Baruwa, ya tabbatar wa INEC cewa wannan yarjejeniyar da su ka sa wa hannu sun amince alƙawari ne cewa za su yi aiki tsakani da Allah domin bai wa ƙasar su gudummawar tabbatar da an gudanar da zaɓukan 2023 cikin kwanciyar hankali.