Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) a jihar Sokoto ta bayyana shirinta na sake gudanar da zaben cike gurbi a rumfunan zabe 46 na jihar.
Zaben na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ta soke wasu zabukan da aka gudanar a jihar, wanda daga baya hukumar zabe ta kasa ta ayyana ranar 3 ga watan Fabrairun 2024 domin sake gudanar da zabe.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ofishin INEC da ke Sokoto, Muhammad Hassan Ka’oje ya raba wa manema labarai a ranar Talata, ta ce, kotu ta bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 46 da ke mazabar tarayya ta Yabo/Shagari, Bodinga ta Arewa da Tambuwal ta yamma.
A yayin da take ba wa al’ummar mazabar da abin ya shafa tabbacin cewa sun shirya tsaf domin tabbatar da kowa ya gudanar da ‘yancin dimokaradiyyar da doka ta tanadar masa, sanarwar ta yi nuni da cewa, wadanda ke da katin zabe na dindindin da suka yi rajista a rumfunan da abin ya shafa ne kadai suka cancanci kada kuri’a a zabukan da za a gudanar.