Mataimakin shugaban cibiyar hasashen yanayi ta kasar Sin Zhang Hengde, ya bayyana cewa, yanayi a kasar Sin ya samu kyautatuwa a shekarar 2022.
Jami’in ya bayyana cewa, a shekarar 2022, matsakaicin alkaluman PM 2.5, alkaluman da ake amfani da shi wajen auna gurbacewar iska, ya ragu da kashi 3.3 bisa 100 a shekara a kasar Sin.
Zhang wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai, ya bayyana cewa, matsakaicin adadin kwanakin da aka yi fama da yanayi na hazo a fadin kasar a bara, ya kai kwanaki 19.1, raguwar kwanaki 2.2 idan aka kwatanta da shekarar 2021.
Zhang ya kara da cewa, daga watan Mayu zuwa Oktoba na shekarar 2022, kididdigar da aka auna yanayin na gurbatar yanayi na laimar ozone, ta karu da kashi 9.7 bisa 100 bisa makamancin wannan lokacin a shekarar 2021, saboda raguwar kwanakin da aka yi ruwan sama da kuma yanayin matukar zafi . (Ibrahim)