Yayin da aka koma makaranta a fadin tarayyar Nijeriya sabuwar domin ci gaba da karatu a shekarar 2025, mutane na nuna damuwa/shakku kan irin ingancin makarantu masu zaman kansu,wato yadda wadanda suka mallaka domin ai sune masu amfani da arha wajen tafiyar da makarantun, manufa irin Malaman da suke dauka da amfani da su ba wasu masu inganci bane don haka sai su rika biyansu albashin d suka dama.
Binciken da LEADERSHIP ta yi ya nuna makarantu masu zaman kansu suna kara bunkasa ko kuma yin yawa saboda bukatar da al’umma suke da ita, ta samun ilimin.Duk da hakan akwai damuwa kan ingancin su Malaman,saboda masu makarantun sun kasa biyansu mafi karancin albashi duk kuwa da yake suna amsar makudan kudaden makaranta masu yawa daga hannun iyayen yara.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kaddamar Da Tsarin Mayar Da Yara Zuwa Makaranta
- Manyan Makarantun Bauchi Sun Tsunduma Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani
An samu labarin cewar makarantu masu zaman kansu na karuwa a Nijeriya musamman ma a Birane.
Binciken da aka yi ya nuna wadanda suke da bukatar ‘ya’yansu su samu wuraren da za su yi karantu sanadiyar rashin gamsuwarsu da, azuzuwa inda ‘yan makaranta suke da yawa a aji daya, makarantun da ba a basu kudaden da suka kamata don tafiyar da kansu, kayan karatu sun lalace, wadannnan dalilan ne suka sa makarantu masu zaman kansu suke kara yawa.
Sai dai kuma yayin da su makarantu masu zamn kansu ke kara samu wurin zama, babbar matsalar ita ce ana da shakku kan ingancinsu musamman ma Malamai a irin wadancan makarantun.
La’akari da yadda makarantu masu zaman kansu ke ta karuwa saboda a samu biyan bukatun wadanda suke son sa ‘ya’yansu makarantun,tambayoyin anan sun hada da ko dai basu damu bane da rashin ilimin muhimmanci ilimin Malamai, da irin takardar shedar ilimin da aka mallaka, sai kuma irin ci gaban kwararrun bangaren ilimi, ko kuma kawai dai sun fi mai da hankali ne kan ci gaban bangaren.
Masu ruwa da tsaki da suka yi hira da LEADERSHIP sun nuna damuwarsu cewa wasu daga cikin makarantu masu zaman kansu suna amfani ne da musamman rashin ilimin da ya dace, suna daukar Malaman da basu kamata ace suna koyarwa ba, suna basu albashin da bai taka kara ya karya ba saboda kawai su sun samu arha.
Damuwar ce da tayi yawa ta sa aka yi muhawara kan minene fifikon tsakanin samun damar yin wani abu, iya yin shi,sai irin ilimi mai inganci da ake koyawa daliban.
A Nijeriya fiye da kashi 80 cikin 100 na makarantun sakandare, makarantu masu zaman kansu ne suka mallake su, yayin da kuma kashi 20 kadai na makarantun ke karkashin gwamnati.
Kamar bayanan da aka samu daga hukumar kula da ilimin makarantun Sakandare (NSSEC), da akwai makarantun Sakandare kamar 50,000 a Nijeriya, masu zaman kansu ne suka mallaki fiye da kashi 80 daga cikinsu.
Ana kuma da labarin cewa abinda ke jan hankalin mutane zuwa kai ‘ya’yansu makarantu masu zaman kansu shi ne irin ilimi mai inganci da ake samu a makarantun masu zamankansu.Yawancin iyaye suna ganin makarantun masu zaman kansu sun yarda da cewa akwai hanya da ke dadadawa iyaye wato yadda suke koyarwar, ga shi basu da yawa a aji, ga kuma kuma manhajar koyarwar ta yi daidai da irin tsarin kasashe na kasa da kasa.
Bugu da kari kuma makarantu masu zaman kansu sun mallaki abubuwan da za su jawo hakalin mutane masu inganci, azuzuwa na zamani, dakin gwaji na komfuta, kayan wasanni, wanda hakan ne yasa ake jan ra’ayin iyalai wdanda za su iya biyan kudin makarantar.
Sai kuma yayin da iyaye ke ta rububin kai ‘ya’yansu zuwa su makarantu masu zaman kansu, kawai sai makarantu suka samu ci gaba na fadada su, ba tare da mai da hankali ba kan irin ingancin Malaman da suke koyarwa a irin makarantun ba. Wakilinmu ya samu labarin yadda ake daukar daukar Malamai ba zai zama mai tsanani ba yawancin makarantu masu zaman kansu,musamman ma wadanda suke kadan ko wadanda za su iya sa ‘ya’yansu a Abuja.
An samu rahoton cewar wasu makarantu masu zaman kansu suna daukar wadanda basu da ilimin koyarwa, ko kuma suna bada albashin da bai taka kara ya karya ba,wanda irin hakan ne bai jan hankalin wadanda suka cancanci su koyar a makarantun saboda rashin albashi mai gwabi.
A Abuja, wani binciken da LEADERSHIP bta yi ya gano ‘yan makarantu kalilan ne suke biyan albashi mai gwabi,suke kuma daukar Malaman da suka cancanta,yawancin makarantu masu zaman kansu su basu da wani zabi lokacin da suke daukar Malamai.
Yawancin makarantu suna a kauyukan da suke makwabtaka ne da Babban Birnin tarayya wadanda kuma mutane masu karamin karfi ke sa ‘ya’yansu.A makarantun, ana biyan Malamai daga Naira 30,000 zuwa 50,000 ko wane wata, abinda yayi kasa da mafi karancin albashi ga yawancin sauran ayyukan.
A makarantun da suka amsa sunansu a cikin Babban Birnin tarayya, suna biyan albashin Malamansu daga Naira 100,000 zuwa 300,000 kowane wata suna kuma da ilimin da ya kamata ace Malamin makaranta yana da shi, kamar yadda wakilinmu ya samo labari daga wurin Malaman makaranta a makarantun Babban Birnin tarayya.
Wani abinda da zai daure kai wasu daga cikin Malaman a irin kananan makarantu masu zaman kansu ba dole bane sai sun kasance suna da shedar ilimin da ta shafi lamarin koyarwa.Tattaunawar da aka yi a makarantu na wasu wurare kamar Lugbe, yawancin Malaman sun bayyana suna da digiri a wasu fannonin da basu da alaka da shi lamarin koyarwa sanin makamar koyarwa na ilimi ba, amma sun shiga harkar ta koyarwa saboda suna bukatar kudi ne domin tafiyar da rayuwarsu.
Ya ce “Na karanta darasin lissafi ne (Mathematics.) Tun lokacin dana kammala aikin yiwa kasa hidima a shekarar 2016,na zo Abuja ne domin in samu ayyuka masu tasiri.Sai dai kuma bada wani bata lokaci bane aikin koyarwa sh ne wanda ba daukar lokaci mai tsawo ake samun shi ga wanda ya kammala jami’a cewar Moses Malami a wata makaranta mai zamankanta,”.
Iyaye ma suna magana kan ko ingancin ilimi yana da alaka da irin kudade masu yawa da su makarantu masu zaman kansu suke amsa daga wurinsu saboda ‘ya’yansu na karatu a makarantun.
Isaac Moji, shi ma mahaifin ne wanda ‘ya’yan shi suka yi makaranta mai zaman kanta a Nyanya, cewa ya yi duk da yake ana maganar ingancin Malami, shi ya fi son ya kai ‘ya’yan shi makaranta mai zaman kanta saboda ajin irinsu bam ai wani girma sosai bane ga kuma kayan koyarwa na zamani da suka dace.
Da yake bada na shi dalilin kna lamarin, Dakta Iyela Ajayi, babban sakatare na hukumar kula da ilimin babbar sakandare (NSSEC),ya yarda da cewa makarantu masu zaman kansu suna bda tasu gudunmawar a bnagaren ilimi, amma yace rashin albashi mai tsoka wadanda yawancin makarantun masu zaman kansu ke biya yana hana Malamai wadanda suka cancanta shiga aikin koyarwa.
“Maganar gaskiya ba zamu iya tafiyar da lamarin b aba tare da makarantu masu zaman kansu ba. A yau, muna da makarantun Sakandare kusan 50,000 a Nijeriya, makarantu masu zaman kansu ne ke da kashi 80 daga cikin 100 na makarantun ,”.
Ya bukaci da kuma yin kira da gwamnati ta maida hankalin ta kan cewa makarantu masu zaman kansu su rika amfani da bin doka ta irin shedar ilimi ake bukata mai son harkar koyarwa ya mallaka, kayan aiki, da kuma manhajar koyarwa mai inganci. Ajayi duk haka ya nuna rashin jin dadin sa yadda ake samun magudin jarabawa a makarantu masu zaman kansu,inda makarantu ke mai da hankali kan koyar da lamarin da ya shafi yin gwaji (test) maimakon samar ingantaccen ilimi wanda ya kamata.