Ranar Talata ce 15 ga Oktoba 2024 gwamnatin tarayya za ta kaddamar ‘da shirin, mai da yara wadanda suka bar zuwa makaranta suke gararanba a cikin gari’ matakin da aka dauka zai bunkasa ilimi a duk fadin tarayyar Nijeriya.
Ministar harkokin mata Mrs. Uju Kennedy, ita ce ta bayyana hakan lokacin da take kaddamar da ‘Jagora kan ilimin ‘ya’ya mata’ taron da kungiyar gwamnonin Nijeriya ta shirya wanda aka yi a dakin taro na fadar Shugaban kasa a, Abuja.
- Yawan Karuwar GDPn Sin Daga Watan Janairu Zuwa Satumban Bana Ya Kai 4.8% Bisa Na Makamancin Lokacin A Bara
- MOFA: Ministan Harkokin Wajen Birtaniya Zai Ziyarci Kasar Sin
Ta bayyana cewar, “Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin fara daukar yara wadanda basu zuwa makaranta masu yawo akan Titi daga ranar Talata 15 ga Oktoba 2024.”
“Idan aka samu dauko irin yaran zai ba gwamnatin tarayya damar haduwa da Iyayensu, musamman ma mata.”
Mrs. Kennedy ta kara jaddada cewa, “Gwamnatin tarayya ta shirya ta taimakawa mata wadanda suka haifi yaran da basu zuwa makaranta, saboda hakan za isa su kara kaimi wajen yadda za su kula da ilimin ‘ya’yansu.”
Shi yasa tayi kira da duk masu ruwa sa tsaki da kuma wasu ‘yan Nijeriya masu da’awar ci gaban ilimin ‘ya’ya mata, su hada kansu domin taimaka wa mata masu karamin karfi a fadin Nijeriya.
Da take jawabi a kan ‘Taimakawa domin abubuwa su yi kyau,’ Sakatariya tsarin shirin ta ma’aikatar harkokin mata, Dayo Benjamin-Olaniyi, ta ja hankalin mutane kan cewa, “Ilimi shine wani ginshikin cigaban al’umma ta bangarori daban-daban, idan kuma ana maganat ilimin ‘ya mace shine mabudin bude hanyoyin cigaban al’umma baki daya‘.”
Ta yi karin haske akan cewa“samun ingantaccen ilimi shine abinda zai ba mata kwarin gwiwa su kasance masu taimaka ma wasu , su fita daga cikin kuncin rayuwa da fatara ke haifarwa, fita daga kangin rashin adalci, a daina nuna masu wariya, su koma wadanda za su rika kawo ma al’ummma sauye- sauyen cigaba.”
Da take bayani akan muhimmancin ilimin ‘ya mace, ta ce shit sarin da za a’ fara amfani da shi zai fitar da mutane da yawa daga kuncin talauci,saboda, “Ya’ya mata da suke da ilimi su ake sa ran su samu ayyuka wadanda ke da albashi mai tsoka, ta hakan za su fita daga fatara da kuma iyalansu.
Da take tsokaci akan samun daidato tsakanin mata da maza ta ce “Ta hanyar ilimi ne za’a samun damar yin hakan wajen kawo karshen duk abubuwan cutarwa ga mata, da samun damar da ba zata taimaka ayi rashin adalci ba.
Hakanan ma ilimi yana taimakawa mata su kasance masu bada gudunmawa ta bangaren da ya shafi lafiyarsu, rage yawan mutuwar mata da kananan yara, su samu kwarin gwiwa ganin za su iya taimakawa mata mata ‘yan’uwansu su kasance jagorori a wuraren da suke.Bugu da kari mata masu ilimi suna bada gudunmawar bunkasar tattalin arziki, samar da abinda zai taimakwa cigaban kasa.”