Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kaddamar da rabon Naira miliyan dari biyar (N500,000,000) a matsayin tallafi ga kungiyoyin ‘yan kasuwa daban-daban a Jihar Gombe don taimaka musu wajen sake inganta sana’o’i da kasuwancin su da kuma shawo kan matsalar tabarbarewar tattalin arziki da annobar Korona ta haifar.
Wannan karimcin na zuwa ne a karkashin shirin farfado da tattalin arzikin Jihar Gombe na COVID-19 da ake kira GO-CARES, wanda shirin tallafi ne na gwamnatin jihar.
Da ya ke jawabi a wajen bikin kaddamar da shirin, gwamnan yakce, gwamnatin sa ta himmatu matuka wajen magance kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da suka addabi al’ummar jihar wanda shi ne dalilin kafa gidauniyar farfado da tattalin arzikin Nijeriya wato NG-CARES na Gwamnatin Tarayya a Jihar Gombe inda aka ware sama da Naira biliyan 8 da miliyan 500 don tallafawa magidanta 288,700 da manoma da masu kananan sana’o’i a lungu da sako na jihar domin dakile barnar da cutar Korona ta yi ga tattalin arzikin kasa da rayuwar al’ummar duniya.
Ya ce, tun bayan kaddamar da shirin a watan Yulin shekarar da ta gabata, shirin na GO-CARES ya kashe kimanin Naira biliyan 3 da miliyan 400 ta hanyar ayyuka daban-daban da kuma tallafin daya kai ga dubban iyalai da ‘yan kasuwa masu rauni.
“Ya zuwa yanzu, ‘yan asalin Jihar Gombe dubu 147 da 666 ne suka ci gajiyar wannan shirin na GO-CARES kuma za a sanya karin wassu da dama nan gaba. Namu tallafi ne ba rance ba, kuma rabon wannan makudan kudade shaida ce ta yadda muke daukar sana’o’i da muhimmanci saboda irin rawar da suke takawa wajen ci gaban jihar mu”.
Gwamnan ya bayyana cewa ajandar ci gaban da gwamnatin sa ke aiwatarwa ta hanyar zurfafa zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa da samar da ci gaban jama’a ya samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa, inda ya bada misali da hanyoyi a rukunin masana’antu na Nasarawo da babbar kasuwar Gombe da fitulun hanya masu amfani da hasken rana da inganta tsaro da sauran su.
Tun da farko a jawabin sa na maraba, kwamishinan ciniki, masana’antu da yawon shakatawa, Hon. Nasiru Aliyu ya ce, gwamnatin Inuwa zata ci gaba da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa don dawo da martabar kasuwanci.
Shi ma a nasa jawabin, kwamishinan Matasa Hon. Abubakar Aminu Musa, ya ce shirin na GO-CARES ya ceto iyalai da ‘yan kasuwa da dama a fadin jihar ta hanyar tsare-tsaren sa daban-daban, inda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin su bada goyon bayan ci gaba da shirin ta hanyar sake zabar Gwamna Inuwa Yahaya a karo na biyu.
Da suke jawabi a madadin ‘yan kasuwan da suka amfana, Alhaji Sunusi Abdullahi Mai Agogo da Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa kafa waje Alhaji Uba Abdullahi da Shugabar Mata ‘yan Kasuwa Dr. Eliza Danladi da Shugaban hadin kan kungiyar ‘yan kasuwa ta Amalgamated, Alh. Abba Bill Gates, sukace Gwamna Inuwa ya cika alkawuran daya dauka na tallafawa ‘yan kasuwa, suna masu godiya bisa wannan karimcin, tare da bada tabbacin yin amfani da tallafin yadda ya kamata.
Sun kuma yi alkawarin ci gaba da bai wa gwamnan goyon baya, tare da yi masa alkawarin zasu ramawa kura aniyar ta a zabe mai zuwa domin dorewar ayyukan raya ƙasa da kuma maslahar Jihar Gombe.