Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Nijeriya (IPMAN), ta kulla yarjejeniya da matatar Dangote don fara dakon man fetur kai-tsaye daga wajenta.
Ana sa ran fara dakon man fetur din zai samar da wadatar man fetur a farashi mai sauki a fadin kasar nan.
- Miji Ya Kone Matarsa Da Fetur Kan Samun Sabani
- Hezbollah Ta Harba Rokoki 165 Zuwa Arewacin Isra’ila – IDF
Shugaban IPMAN, Abubakar Shettima-Garima ne, ya sanar da cimma yarjejeniyar, inda ya jaddada amfaninsa ga wadatar man fetur da kuma bunkasar kudin shiga ga Nijeriya.
Ya bukaci dukkanin mambobin IPMAN su bai wa matatar Dangote goyon baya don samar da makamashi mai dorewa ga ‘yan Nijeriya.
Shettima-Garima ya kuma yaba da kokarin Shugaba Tinubu wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, tare da jaddada shirye-shiryen IPMAN na tallafa wa manufofin gwamnati, ciki har da fadada ababen hawa masu amfani da gas.