Biyo bayan sabuwar takaddama na sayen tataccen mai daga matatar Dangote, kungiyar dillan mai ta kasa IPMAN, ta sanar da cewa, ta na kan tattaunawa da matatar Dangote, dangane da fara sayen mai, daga matatar ta Dangote.
Shugaban rukunin matatar man Dangote Alhaji Aliko Dangote, ya yi zargin cewa, kamfanin kula da albarkatun main a kasa NNPCL, tare da sauran masu ruwa da tsaki, suna shigo da man daga wasu kasashen duniya, suna kuma kin sayen wanda matatarsa ke tacewa.
- Karin Kayayyaki Daga Kasashe Mafi Karancin Ci Gaba Sun Shiga Kasuwar Kasar Sin Ta Bikin CIIE
- Zargin Cin Zarafin Likita: Gwamna Yusuf Ya Roki Likitoci Su Bayar Da Kofar Sulhu
Dangote ya kara da cewa, matatarsa, na da karfin da za ta iya samar da tataccen man lita miliyan 500.
Sai dai, a martanin da mai magana da yawun IPMAN na kasa Cif Chinedu Ukadike, ya bayyana cewa, kungiyar ba ta riga ta sayo man daga matatar Dangote ba, domin har yanzu, ana ci gaba da tattaunawa a kan batun.
A cewarsa Chinedu,“Har yanzu, bamu karbi kayan daga matatar man ta Dangote ba, amma ana ci gaba da tattaunawa za mu nkuma sanar idan mun fara karbar kayan daga matatar.”
A daya bangaren Chinedu ya bayyana cewa, karin farashin mai da kamfanin NNPCL bayan kwanuka biyu, ba abin mamaki bane duba da yadda kasuwar ta kasance.
Sai dai, duk da karin Naira 30 na kowacce Litar mai daya, wanda ya kai kaso 3 a cikin dari zuwa Naira 1, 060 na kowacce lita daya a Abuja, dilallan man sun ci gaba da sayar da man a watan Okotobar 2024 a kan farasahin da take sayarwa.
Wani bincike da Jaridar Banguard ta gudanar ya nuna cewa, manyan dillalan man kamar su, Conoil and TotalEnergies, sun ci gaba da sayar da man su a kan farashin Naira 1,109, NIPCO akan farshin Naira N1,115, Adoba Plc a kan Naira N1,125, inda kuma akasarin dilalan man, ke sayar da man a kan Naira 1,150 – N1,230.
A kwannan baya ne NNPC ya kara farashin wanda ya kai kashi 14.8 a ranar 9 ga watan Okotobar, 2024, inda karin farashin man ya kai daga Naira 897 zuwa Naira to 1, 030 na kowacce lita daya, bayan cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi.
Wannan karin ya sabawa tunanin yarjejiya a tsakanin gwamnatin tarayya da matatar man Dangote, na sayar da danyen mai a farashin Naira mai makon da farashin dala wanda hakan ya sanya farashin ya fara raguwa a ranar 1 ga watan Oktobar 2024.
Karin na kwanan nan, da aka yi a ranar 3 ga watan Satumbar 2024 ya faru ne, bayan NNPC, ya kara farashin litar man zuwa kashi 45, inda farashin ya karu daga Naira 617 zuwa Naira to 897 na kowacce litar man daya.