Ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) ta bayyana cewa, za a fara sayar da litar mai kan Naira 935.
Wannan ya biyo bayan rage farashin mai da matatar Dangote ta yi wa dillalan man.
- Yawan Kai-Komon Mutane Tsakanin Lardunan Sin Zai Kai Kimanin Biliyan 64.5 A 2024
- Saka Zai Yi Jinyar Makonni Bayan Raunin Da Ya Samu
Shugaban ƙungiyar IPMAN na ƙasa, Maiganfi Garima, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), cewa rage farashin man ya zama dole domin bai wa dillalai damar sayar da mai kan farashi mai sauƙi ga jama’a.
A ranar Alhamis da ta gabata ne, matatar Dangote ta rage farashin man daga Naira 970 zuwa Naira 899.50 ga dillalai, wato ragin Naira 70.5 a kowane lita.
Wannan matakin, a cewar matatar, na da nufin sauƙaƙa wa jama’a yayin bukukuwan ƙarshen shekara da kuma rage farashin sufuri.
Rahotanni sun nuna cewa an fara ganin tasirin wannan ragi a Legas, kuma ana sa ran sauran jihohin ƙasar za su fara ganin canji daga ranar Litinin.
Haka kuma, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC), ya rage farashin litar mai daga Naira 1,020 zuwa Naira 899 ga dillalai.
Ana ganin wannan ragin farashi ya samo asali ne sakamakon ƙarin matatun mai da ke samar da man fetur a ƙasar da kuma gasar kasuwanci da ke tsakanin NNPC, Dangote, da sauran dillalai.