• English
  • Business News
Tuesday, November 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iran Da Isra’ila Sun Amince Su Tsagaita Wuta – Trump

by Sadiq
5 months ago
Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce Iran da Isra’ila sun amince su dakatar da yaƙi a tsakaninsu.

Ya sanar da haka ne a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce Iran ce za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani kuma Isra’ila za ta bi sahu.

  • Majalisar Dattawa Na Nazarin Shawarwari 31, Da Ƴancin Ƙananan Hukumomi
  • Likitocin Kasar Sin Sun Gudanar Da Ayyukan Kiwon Lafiya Kyauta Ga Yara A Botswana

A halin yanzu dai Isra’ila tana ci gaba da kai hari kan Iran, kamar yadda ministan tsaronta ya faɗa, yayin da Iran ta gargaɗi mutanen garin Ramat Gan kusa da Tel Aviv da su bar wajen saboda yiwuwar kai hari.

Trump ya ce tsagaita wutar za ta fara aiki cikin awa shida, kuma daga nan zuwa awa 24 yaƙin zai ƙare gaba ɗaya.

Shin sun tsagaita da gaske?

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Sai dai babu wani tabbaci daga gwamnatin Iran ko Isra’ila kan cewa sun yarda su dakatar da yaƙin.

Trump ya kira rikicin da ake ciki da suna “yaƙin kwana 12,” yana mai cewa wannan rikici da za a iya yin shekaru ana fafatawa da shi bai bazu ba, kuma ba zai bazu ba.

Mene ne ke faruwa yanzu?

Bayan da Trump ya sanar da cewa an tsagaita wuta, Isra’ila ta ce an kashe mutane uku sakamakon hare-haren da Iran ta kai.

Amma ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce babu wata yarjejeniya ta tsagaita wuta.

Sai dai ya ce Iran za ta daina kai hari idan Isra’ila ma ta dakatar da nata.

Rikicin ya tsananta ne bayan Iran ta kai hari sansanin sojin Amurka da ke Qatar, wanda ya sa Trump ya nemi a dakatar da faɗan.

Me Iran da Isra’ila suka ce?

Gidan talabijin na Iran (IRINN) ya ce an tsagaita wuta ne bayan da Iran ta samu nasara a harin da ta kai.

Sun ce Trump ne ya roƙi a daina faɗam.

Ministan harkokin wajen Iran ya ce Iran ta daina kai hari tun ƙarfe 4 na dare, idan har Isra’ila za ta daina nata.

Har yanzu Isra’ila ba ta fitar da wata sanarwa ba kan tsagaita wutar, sai dai bayan sanarwar Trump, Isra’ila ta sake kai hari Iran.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Muka Zama Bayin ‘Yan Bindiga -Mazaunin Wani Kauye
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina

November 11, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo
Manyan Labarai

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

November 10, 2025
Next Post
Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 600 Cikin Mako 3

Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 600 Cikin Mako 3

LABARAI MASU NASABA

Yadda Muka Zama Bayin ‘Yan Bindiga -Mazaunin Wani Kauye

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 2 A Ƙauyen Katsina

November 11, 2025
An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

An Daddale Kulla Cinikin Sama Da Dala Biliyan 83 A Bikin CIIE Na Kasar Sin 

November 10, 2025
Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

Kamfanonin Kasa Da Kasa Na Fatan Yin Amfani Da Damammaki Na Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar–Biyar Karo Na 15 Na Sin

November 10, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata 4 Masu Shayarwa, Da Shanu 50 A Kano

November 10, 2025
Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

Sin Ta Dakatar Da Jiragen Ruwan Amurka Daga Biyan Kudi Na Musammam A Tashoshinta Na Ruwa

November 10, 2025
Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

Sin Ta Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Masu Zagaye Kusa Da Doron Kasa

November 10, 2025
Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

Babban Dalilin Da Ya Sa EFCC Ke Naman Tsohon Minista Ruwa A Jallo

November 10, 2025
Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Ci Gaba Da Bude Kofa Mai Zurfi A Sin

November 10, 2025
Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

Gwamnati Ta Nemi Ƴan Nijeriya Su Ƙwantar Da Hankali Kan Barazanar Trump

November 10, 2025
Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo

Mataimakin Firaministan Kasar Sin Zai Ziyarci Kasashen Guinea Da Saliyo

November 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.