Matakin da Iran ta dauka na harba makamai masu linzami masu hanzarin da ya kai 180 a Isra’ila na nuni da cewa Tehran ya yi mummunar barna a harin da aka kai a daren ranar Talata, sabanin harin da aka kai da makami mai linzami a watan Afrilu.
Gudun da makaman suke ya sa makaman ballistic suka yi kakkabo su, amma dai rahotannin farko na nuni da cewa ba a samu asarar rai ba cikin Isra’ila da gabar yammacin kogin Jordan, duk da yawan makaman da aka harba.
- Tinubu Ga ‘Yan Kasa: Ina Sane Da Tsadar Rayuwar Da Kuke Ciki
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Rage Kudin Sufuri Da Kashi 40 Ta Hanyar Amfani Da Motoci Masu Iskar Gas
Makamai masu linzami samfurin Tehran Emad da Ghadr, da aka yi amfani da su a farkon wannan shekara, an kiyasta gaggawar tafiyarsu ya ninka sau shida ko fiye da haka, sannann minti 12 kacal suka dauka daga Iran zuwa Isra’ila. Wannan haura fiye da makamain 4,600mph. Amma Iran ta ce ta aika da makami mafi gaggawa Fatteh-2, tare da 10,000mph mai matsakaicin sauri kamar yadda aka kiyasta.
An yi kiyasin cewa Iran tana da makaman roka kusan 3,000 samfurin ballistic, ko da yake Amurka ta yi lissafin haka ne shekaru biyu da rabi da suka gabata, don haka adadin zai iya karuwa. Tehran za ta so ta ci gaba da rike mafi yawan hannun jarin ta idan har rikici da Isra’ila ya kara ruruwa zuwa babban yaki.
An harba makamai masu linzami da yawa a cikin ‘yan mintuna da za su yi wahala su riski inda ake bukata a Isra’la, Saboda suna da kwarewa wajen harbo makami mai linzami.
Dakatar da makamin ballistic a cikin jirgin babban aiki ne na da Arrow 3 na Amurka-Isra’ila ke da alhakin dauka tare da mai nisa Arrow 2, wanda aka fara amfani da shi a lokacin yakin Isra’ila da Hamas, na Dabid’s Sling matsakaicin zango ke tallafawa.
A watan Afrilu, wani tsohon mai ba da shawara kan harkokin kudi ga shugaban ma’aikatan IDF ya ce makami mai linzami na Arrow yawanci kudinsa ya kai Dala miliyan 3.5 daidai da Fam miliyan (£2.8m), a lokaci guda, kuma Dabid’s Sling mai kakkabo makami kuma kudinsa ya kai Dala miliyan $1m daidai da Fam (£ 800,000).
Harbo makamai masu linzami 100 ko fiye zai iya shiga cikin sauƙi zuwa daruruwan miliyoyin daloli – ko da yake makamai masu linzami da kansu za su ci Iran fam 80,000 kowanne ko fiye da haka.
A wancan lokacin, Ministan Harkokin Wajen Tehran, Hossein Amir-Abdollahian, ya ce ta bai wa kasashen da ke makotaka da kasar sa’o’i 72 na sanar da kai harin da aka shirya – wanda ya faru makonni biyu bayan da Isra’ila ta kai harin bam a ofishin jakadancin Iran da ke Damascus. A wannan karon, Iran ta dauki matakin ne a cikin kwanaki da Isra’ila ta kashe shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah a ranar Juma’a.
…Ana Ci Gaba Da Gwabzawa A Kudancin Lebanon
Rahotanni sun bayyana yadda ake ci gaba da gwaba yaki a tsakanin Israíla da dakarun kungiyar Hezbullah a Kudancin Lebanon inda Isra’ila ta ce an kashe mata sojoji guda takwas a ranar Talata.
Israíla ta kaddamar da farmaki ta kasa a kudancin Lebanon kan kungiyar Hezbollah, lamarin da ke kara rura rikicin da ke barazanar barkewar yaki a yankin.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta sun kai farmaki a kauyuka kusa da kan iyaka, yayin da jiragen yaki ke ci gaba da luguden wuta a Lebanon.
Wannan ya biyo bayan illar da Isra’ila ta yi wa Hezbollah, ciki har da kisan shugabanta Hassan Nasrallah.
Duk da cewa an yi wa Hezbollah illa, amma ta jajirce. Kungiyar ta ci gaba da harba rokoki zuwa arewacin Isra’ila kuma ta ce a shirye take ta abka yaki.
Wakilin BBC a Gabas ta Tsakiya Hugo Bachega Beirut ya ce Lebanon ta tashi ne da sabon labarin cewa Isra’ila ta kaddamar da farmaki ta kasa a kudanci.
Fargabar ita ce wannan zai iya zama babbar manufa ta yakar Hezbollah, da ta shafe wata tana yaki da Isra’ila a shekarar 2006.
A wata sanarwa, rundunar sojin Isra’ila ta ce dakarunta tare da taimakon jiragen yaki da makaman atilare sun fara kai farmaki kan Hezbollah a kauyukan da ke kan iyaka, tana mai cewa sun kasance barazana ga al’ummar Isra’ila da ke arewaci.
Ba a dai san yadda yakin zai kaya ba domin fargabar da ake ta nunawa na ruruwan wutar yakin a yankin gabas ta tsakiya tun daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da munanan hare-hare a Gaza.
Kaddamar Da Hari Kan Isr’ila
Rundunar sojin Isra’ila ta ce Iran ta kaddamar mata da hare-hare na makamai masu masu linzami.
Sanarwar da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ta ce hare-haren sun fito ne daga Iran.
Iran ta tabbatar da kaddamar da hare-haren kan Isra’ila, kamar yadda Kamfanin Dillacin Labaran kasar IRNA ya tabbatar.
Isra’ila ta bukaci ‘yan kasarta su kasance cikin shiri tare da neman wurin fakewa idan har sun ji kara ta gargadi.
Masu aiko da rahotanni sun ce an kakkabo wasu makaman a sararin samaniyar Jordan.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce harin makamai masu linzami kusan 100 Iran ta harbo.
Sai dai rahotanni sun ce Amurka ta taimaka wa Isra’ila wajen kakkabo makaman kafin isa Tel Abib.
Bayanai sun ce wasu makaman da Iran ta harbo sun fada yankunan Falasdinawa
A wani labarin kuma, an harbe mutum shida a wani hari da aka kai a Tel Abib, inda akalla wasu mutum bakwai kuma sun jikkata, da dama daga cikinsu sun samu munanan raunuka.
‘Yan sanda sun ce harin ya auku ne a kusa da tashar jirgin kasa da ke yankin Jaffa na birnin.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce maharan biyu da aka gani suna sauka daga jirgin kasa, wani mai wucewa ne da kuma wani mai gadi ne suka harbe su.
Hotunan sun nuna daya daga cikin maharan dauke da bindiga.
Zuwa yanzu ba a san dalilin kai harin ba.