Kungiyar Liverpool ta cimma yarjejeniya da Newcastle domin ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙasar Sweden, Alexander Isak, akan zunzurutun kuɗi fam miliyan 125, wanda zai sanya shi zama ɗan wasa mafi tsada a tarihin gasar Firimiyar Ingila. Rahotanni sun bayyana cewa Isak zai yi gwajin lafiya yau Litinin tare da zakarun Firimiya, kafin a kammala sanarwar a hukumance da misalin ƙarfe 7 na yamma.
- Al Hilal Za Ta Biya Yuro Miliyan 53 Don Ɗaukar Nunez Daga Liverpool
- Liverpool Za Ta Kece Raini Da Bournemouth, Arsena Za Ta Bakunci Man Utd A Wasan Mako Na Firimiya Ta Baɗi
A farkon tattaunawar, Newcastle ta dage cewa sai Liverpool ta biya fam miliyan 130 kafin ta sayar da ɗan wasan, amma daga bisani aka amince da fam miliyan 125. Wannan mataki ya biyo bayan kwantiragin shekaru shida da Isak ya amince da shi a baya, inda ya nuna sha’awarsa ta komawa ƙungiyar mai horaswa Arne Slot.
Tun lokacin bazara Liverpool ta fara zawarcin Isak, inda ta fara da tayin fam miliyan 110 da Newcastle ta ƙi amincewa da shi. Bayan tattaunawa mai tsawo, ƙungiyar ta cimma nasarar da take nema, yayin da Newcastle ta yanke shawarar siyar da ɗan wasan don buɗe hanya ga ɗaukar matashin ɗan wasan Jamus, Nick Woltemade.
A cewar rahotanni, Liverpool za ta miƙa riga mai lamba 9 ga Isak, wanda hakan zai ƙara ɗaukaka matsayin sa a ƙungiyar. Idan aka kammala yarjejeniyar, zai kafa tarihi a matsayin ɗan wasan da aka fi kashe kuɗi akansa a gasar Firimiya, alamu kuma sun nuna cewa sanarwa a hukumance daga kungiyar na nan tafe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp