A ranar Laraba, gobara ta kone mutane hudu a dangi ɗaya a wani gida da ke Kundila Layin Baba ‘Imfosibul’ a karamar hukumar Tarauni ta jihar Kano.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, ACFO Saminu Yusif ya sanya wa hannu, inda ya ce, ɗaya daga cikin ma’aikatanta, HFS Abba Datti ne ya bayar da rahoton gobarar da misalin karfe 4:13 na safiya.
- Sin Ta Sanar Wa WTO Kan Yadda Ta Kulla Yarjejeniyar Bunkasa Huldar Abota Ta Yin Hadin Gwiwar Tattalin Arzikinta Tare Da Afirka
- Tinubu Ya Ɗage Tafiyarsa Zuwa Taron G20 Bayan Hare-haren Kebbi Da Kwara
A cewarsa, da isowar jami’an hukumar, gobarar ta riga ta mamaye gidan, wanda ke da ɗakunan kwana biyu, falo, kicin da bayan gida.
Sanarwar ta bayyana cewa, gobarar ta rutsa da mutane biyar ne a cikin gidan – ciki har da mahaifi mai shekaru 43, Shodandi; matarsa, Rafi’a, mai shekaru 30; da ‘ya’yansu mata biyu – Mardiya mai shekaru 3 da Yusira mai shekara daya da rabi – dukkansu sun mutu.
Hukumar ta kara da cewa, jami’anta sun ceto wani yaro mai shekaru 12, mai suna Aminu Shodandi.
Hukumar ta jajanta wa iyalan da suka rasu ta kuma gargadi al’umma da su ci gaba da kula da abubuwan da ka iya haddasa gobara musamman a wannan lokacin na hunturu.














