Ibeadua Judith Chioma ba ta taba tunanin za ta je makaranta ba a rayuwarta kuma ta auri mutumin da take so, balle ma ta haifi ‘ya’ya.
Ta yi wannan tunanin ne saboda matar, mai shekara 31, na da nakasa kuma iyayenta sun rasu tun tana ‘yar shekara shida.
- Da Dumi-Dumi: Jami’an Tsaro Sun Kai Samame Gidan Tukur Mamu
- Saudiyya Ta Ja Kunnen Netflix Kan Yada Fina-Finan Da Suka Keta Dokokin Musulunci
Judith, wadda ba ta dade da kammala bauta wa kasa a Nijeriya ba (NYSC), ta ce ‘yan mata irinsu suna zuwa makaranta ne kawai idan ba su samu namijin da za su aura ba.
Lokacin da mijinta ya fada wa iyayensa niyyarsa ta auren Judith sai da suka taru suka lakada masa duka har ma suka raunata shi, in ji matashiyar.
‘Ba da lalura aka haife ni ba’ “Ina ‘yar shekara hudu na rasa kafafuwana kuma na gano ba zan iya tafiya ba. Ban san abin da ya faru ba, iyayena za su iya ba da labari amma kuma sun rasu tun ina ‘yar shekara shida,” kamar yadda Judith ta bai wa BBC Pidgin labarinta.
Lokacin da iyayenta suka rasu, sai yayarta ta ci gaba da kula da ita kuma ta kai ta makaranta tun daga nazire har zuwa aji uku na karamar sakandare. “‘Yar uwata ce ta dauke ni, ta ci gaba da koya min abubuwa.
Da rarrafe nake zuwa makaranta da coci, na yi ta kuka ina tambayar Allah me ya sa ya yi ni haka cikin irin wannan halin,” in ji ta.
Gwara na mutu da na yi bara a kan titi in ji gurguwa mai sana’ar dinki Lokacin da take JSS1 ne wani malamin Kirista ya saya mata keken guragu.
Bayan ta kai JSS3 kuma sai shugaban makarantar tasu ya ba da shawarar a kai ta makarantar masu bukata ta musamman.
A nan ne rayuwarta ta fara kyautata. Ta hadu da mutanen da rayuwarta ta fi tasu dama-dama, a nan din ne kuma ta hadu da mijin da ta aura.
‘Duk da wuyar da mijina ya sha bai guje ni ba’ Sun hadu da mijinta gaba da gaba a karon farko bayan sun shafe shekara biyu suna magana ta wayar salula.
Damuwar mijin nata da dan uwansa da ya hada su ita ce; ta yaya za ta iya aikin gida da haihuwar yara da kuma karatu bayan iyayensa sun ki amincewa da auren.
Har ma sai da wasu ‘yan uwansa suka doke shi.
Amma a yanzu tana godiya da farin cikin cewa mijin nata bai guje ta ba. “Lokacin da mijina ya ce zai aure ni mahaifiyarsa ta kira mutane don su taimaka mata a zane shi saboda shi kadai ne danta namiji. Suka zane shi sosai har suka raunata shi,” in ji ta.
“Amma duk da wahalar da ya sha bai guje ni ba.”
Ta kara da cewa abin da suka fi damuwa da shi shi ne yadda za ta dauki ciki, idan ma za ta dauka din.
Yanzu haka ta haihu ba cikin sauki ba tare da wata tiyata ba.
Aure, karatu da sauran kalubale Bayan aurensu, mijinta ya shawarce ta ta ci gaba da karatu.
Ta yi aure ne tana ajin ND 2 kuma tana da ciki.
Ta karanci fannin koyarwar kwamfuta wato Computer Education a kwalejin kimiyya, inda ta kammala bayan shekara shida saboda annobar Korona.
“Na samu gurbi a 2015. Na yi karatun shekara shida saboda annobar Korona. Duk da cewa burinta shi ne ta karanta harkar likitanci, “Amma lokacin da muka fara karatun sai suka ce ba sa daukar masu nakasa a sashen likitanci”.
Mun ciro wannan Rahoto daga BBC