• English
  • Business News
Saturday, May 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iyayena Ba Su Kalubalanci Shigata Harkar Fim Ba —Hadiza Kabara

by Rabi'at Sidi Bala
2 years ago
in Nishadi
0
Iyayena Ba Su Kalubalanci Shigata Harkar Fim Ba —Hadiza Kabara
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Fitacciyar Jarumar fina-finan hausa dake masana’antar kannywood HADIZA MUHAMMAD wadda aka fi sani da HADIZA KABARA, ta bayyana irin kalubalen da suka fuskanta sama da shekara ashirin kafin shigarsu cikin masana’antar Kannywood, har ma da bayan shigar su, ta kuma yi bayani dangane da wasu abubuwan da suka shafi rayuwarta da kuma sana’arta ta fim. Ga dai tattaunawar tare da wakikiyarmu RABI’AT SIDI BALA kamar haka:

Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki, tare da sunan da aka fi saninki da shi.
Sunana Hadiza Muhammad Sani, wadda aka fi sani da Hadiza Kabara, a yanzu kuma an fi sani na da Lantana ko Hauwan dan Badamasi.

Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinki.
Ni haifaffiyar Kano ce, an haife ni a unguwar Yakasai wajen masallacin Jalli, daga nan iyayena aiki ya dawo da su Chalawa wajen Fanshekara. Na yi makarantar firamare a ‘Panshekara Special Primary School’, daga nan na zo na yi makarantar sakandare a ‘Gov. Girls Arabic Secondary School’ Babura. A yanzu ba ni da aure ina tare da yarana guda biyu, wannan shi ne a takaice.

Wanne rawa kike takawa a cikin masana’antar Kannywood?

hadiza kabara
A yanzu dai ina taka rawa kala-kala, ko kuma na ce yanzu tunda girma ya zo mun manyanta, kin san ‘industry’ din da sanda muke ciki mu ne yaran a shekaru can kusan goma sha da suka wuce, ko na ce ashirin ma, mu ne yara. Toh! kuma mu ne iyayen yaran, akwai kakanninmu yanzu, yanzu mu ne iyaye, ina taka rawa matsayin uwa.

Labarai Masu Nasaba

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje

Bangaren shirya fim ko makamancin haka fa?
Yanzu dai na fi karfi a kan matsayin Jaruma, ni Jaruma ce yanzu.

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma harkar fim?
Abin da ya ja hankalina shekaru masu yawa akwai wani tsohon fim din sarauniya wato Allura da Zare, dan sarauniyar na biyu ce. Akwai sarauniya ta gwammaja, akwai wani fim dinsu na Allura da Zare, ina kallo-ina kallo, bayan na gama ‘Secondary School’, sai na zo na shiga ‘Industry’. Toh! akwai wani dan uwana shi yana harkar, na ma ganshi a fim din sai na yi masa magana, ya ce; “Toh! ba matsala tunda iyayenki suka yarda to za a iya kai ki”. Toh! wannan fim din ya yi matukar birge ni, kuma na ga an fadakar shiyasa na ga bari na shiga, da yardar Allah dana fada kuma sai ba samu yadda nake so.

Ya gwagwarmayar shiga masana’antar ta kasance, kamar yadda za ki ga wasu da kuka da shigar?
Mu dai lokacin da muka shiga ‘Industry’ din a lokacin aka buga gwagwarmaya, ba ma ‘yan wasan sosai a lokacin, musamman ma bangaren mata. Lokacin da muka zo ‘industry’ din ma yawanci Maza ne ma suke dan shigar Mata, mu lokacin ba mu da yawa ba mu fi ‘yan tsiraui ba, ba mu fi mu hudu ko biyar ba. Mun zo mun samu Fati Muhammad da Allah ya ji kan rai Hauwa Ali Dodo, sai wata Hasiya Aya, lokacin ma sai dai a ce su ne ‘yan matan. Kin san Hauwa Ali Dodo ba rol din da ba ta bugawa Allah ya ji kan rai. Toh! Sanda muka zo kafin ma a yarda a fara samu a fim din ma mun dan sha wuya, sai mun je ‘location’ din ma sai a ce kai mu tafi gida mun yi kankanta, ko kuma dai “iyayenku sun yarda?”. Toh! Mun samu kalubale kala-kala, kafin Allah ya lamunce mana, yanzu ga shi nan muna cikin harkar da yardar Allah.

hadiza kabara

Lokacin da kika fara cin karo da kalubalen cikin masana’antar ba ki ji kamar ki hakura ba?
Ai duk wata harka da ba za ka hadu da kalubale ba, toh! ka san ba nasara a cikinta, duk abin da ba za ka hadu da kalubale ba, kai ma ka kuka da kanka ka san ba nasara, gwara ka janye ka sake sana’a. Mun fuskanci kalubale kala-kala, amma wannan abun bai sa mun ja baya ba, jajircewa muka yi, amma kalubale mun hadu da shi kala-kala, amma kuma duk da hakan ban taba jin zan fita daga masana’antar ba, sabida ina son abun, ina son aikin kuma Allah ya taimake ni.

Bayan da kika yi nasarar samun shiga cikin masana’antar ya kika ji a lokacin?
A lokacin dana samu kaina a cikin masana’anta ba ni da wayo, irin abin da na ji ma ba zan tantance ba yanzu gaskiya, saboda abin ya dade sosai.

Bayan da kika shiga cikin masana’antar, ko akwai wani kalubalen da kika kara fuskanta?
Kalubale na fada a baya na fuskata kala-kala, wasu ma ni ba zan iya tuna su ba, wannan sirri ne na barwa zuciyata.

Toh! ya batun iyaye fa, lokacin da kika sanar musu kina son shiga, shin kin samu wani kalubale daga gare su?
A’a! Kwata-kwata ni ban samu ba, ban samu kalubale ba wajen iyayena, addu’a suka bini da shi, kuma shi ne na tabbatar addu’ar ce take ta bi na. Ka san ‘by the time’ din da danka ya zo maka da abu ka nuna ina! aka hau wani tashin hankali da sauransu, idan har iyaye ba su sa maka hannu ba, ko ba su yi maka addu’a ba toh ka hakura da abun. Toh! ni sa Allah ya taimake ni adduarsu’a suka bi ni da shi.

Daga lokacin da kika fara kawo iyanzu, za ki yi kamar shekara nawa?
Daga lokacin dana fara fim kawo iyanzu, zan yi kamar shekara ashirin ko ashirin da wani abu.

Da wanne fim kika fara, kuma wanne rawa kika taka cikin fim din?
Na fara da wani fim ne me suna ‘MALAM KARKATA’, sau biyu na fito a fim din, ni har yanzun ma ban taba ganin fim din ba, bai fita ba. Daga baya aka zo aka yi mun wani fim ‘HUKUNCI’, aka zo aka yi mun ‘DABI’A’. Wannan DABI’A shi ne dai kowa ya sanni da shi, amma fim dina na farko shi ne; ‘MALAM KARKATA’. An debo irin wanda suka zo wajen boka neman taimako, toh fita biyu nayi a wannan fim din. Shi kuma HUKUNCI ni ce me jan fim din, dana fito a budurwa da saurayi.

hadiza kabara

Ko za ki iya tuna yawan adadin fina-finan da kika yi?
Gaskiya ba wani abu da zan iya tunawa wallahi, na san dai kawai na yi da yawa yadda ba ma za su misaltu ba.
Za mu ci gaba


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Jarin Kasar Sin Kan Ababen More Rayuwa Ya Gaggauta Ci Gaban Nahiyar Afrika 

Next Post

Ganduje Ya Jajanta Wa Rundunar ‘Yansandan Kano Kan Gobarar Da Ta Tashi A Ofishinta

Related

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe
Nishadi

Ya Kamata Mata ‘Yan Fim Su Rike Mutuncin Kansu – Aisha Tafida Gombe

6 days ago
Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
Nishadi

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje

2 weeks ago
Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda
Nishadi

Daga Kaina An Gama Harkar Fim A Zuri’ata – Moda

2 weeks ago
Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri
Manyan Labarai

Rarara Zai Angwance Da Aisha Humaira Yau A Maiduguri

2 weeks ago
Jerin Manyan Jaruman Fim Da Nijeriya Ta Rasa A Yan Shekarun Nan
Nishadi

Jerin Manyan Jaruman Fim Da Nijeriya Ta Rasa A Yan Shekarun Nan

3 weeks ago
Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?
Nishadi

Me Ya Janyo Jifan Mawaka A Arewacin Nijeriya?

4 weeks ago
Next Post
Ganduje Ya Jajanta Wa Rundunar ‘Yansandan Kano Kan Gobarar Da Ta Tashi A Ofishinta

Ganduje Ya Jajanta Wa Rundunar 'Yansandan Kano Kan Gobarar Da Ta Tashi A Ofishinta

LABARAI MASU NASABA

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

May 9, 2025
Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

May 9, 2025
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

May 9, 2025
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

May 9, 2025
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

May 9, 2025
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.