Ya zuwa ranar Alhamis 11 ga watan nan, lokacin da aka kammala taron baje kolin kasa da kasa na hada-hadar zuba jari da cinikayya na kasar Sin karo na 25, an riga an sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da ayyukan zuba jari a sassa daban daban da yawansu ya kai 1,154, tare da tsara shigar da jarin da ya kai kudin Sin yuan biliyan 644.
Yayin taron, tarin kusoshin manyan kamfanonin kasa da kasa sun shaida cewa, har kullum kasar Sin ta zamo wuri da aka fi aminta da shi ta fuskar zuba jari da samar da ci gaba tsakanin sassan duniya.
Game da hakan, shugaban kungiyar bunkasa cinikayya ta Amurka dake kudancin kasar Sin Harley Seyedin, ya ce wani binciken jin ra’ayoyi da aka gudanar a farkon shekarar nan, ya nuna kaso 76 bisa dari na kamfanoni membobin kungiyar sun sha alwashin zuba dumbin jarin kudade, da shirin fadada hada-hadar kasuwancinsu, tare da inganta ikonsu na gudanar da harkoki a Sin cikin shekarar nan ta 2025.
Kazalika, wasu kamfanoni membobin kungiyar sun riga sun yi kasafin kudaden da suka haura dala biliyan 14.5, tare da fatan kara adadin jarin da suka zuba a kasar Sin cikin shekaru uku zuwa biyar masu zuwa. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp