Jakadan kasar Sin mai kula da harkokin kwance damara, Shen Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasashen duniya su inganta fasahar kirkirarriyar basira ta AI da kyakkyawan nufi kuma ta zama ta kowa da kowa ta hanyar yin shawarwari da hadin gwiwa.
Shen ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar taron duniya kan batutuwan fasahar AI, da tsaro da da’a na shekarar 2025 wanda cibiyar binciken kwance damara ta Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar.
- Ƴansanda Sun Kama Wanda Ya Kashe Ɗan Bijilanti A Tawagar Sarki Sunusi II
- Girgizar Kasa: Shugaban Kasar Myanmar Ya Mika Godiya Ga Tawagar Likitocin Yunnan Ta Kasar Sin
Ya bayyana cewa, ya kamata al’ummomin kasa da kasa su mai da hankali kan samar da ci gaba da inganta tsaro, tare da ci gaba da daukaka tsarin tafiyar da harkokin duniya a game da fasahar AI, ta hanyar karfafa tattaunawa da hadin gwiwa, da karfafa amincewa da juna, da samar da daidaito, tare da inganta manufar AI da kyakkyawan nufi kuma ta zama ta kowa da kowa.
Taron na kwana biyu da aka fara a birnin Geneva na kasar Switzerland a ranar Alhamis da ta gabata, ya tattaro jami’an diflomasiyya, da kwararru daga bangaren sojoji, da masana’antu, da jami’o’i, da kungiyoyin fararen hula da kuma dakunan bincike, inda suka mai da hankali kan yadda ake tafiyar da harkokin fasahar AI a fannin sha’anin tsaro. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp