A ranar 20 ga wata ne jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya Mr. Cui Jianchun ya kai ziyara ta musamman hedikwatar rundunar sojin sama na kasar domin yabawa kan yadda dakarun rundunar suka ceto wasu ’yan kasar Sin su 7 da masu garkuwa da mutane suka sace yau watannin 6 da suka gabata.
A yayin ziyarar jakadan kasar Sin ya samu ganawa da baban hafsan rundunar Air Marshal Oladayo Amawo inda mika godiyarsa.
Mr. Cui Jianchun ya bayyana nasarar da aka samu bisa irin jajircewa da kwazon babban hafsan wajen gudanar da harkokin rundunar.
Ya ci gaba da cewa babu shakka irin gwarzantakar da dakarun musamman suka nuna yayin samamen wanda har ta kai su ga ceto wadannan mutane 7 abin a yaba ne matuka kuma sun nuna kwarewa sosai.
Da yake jawabi babban hafsan sojin sama na Najeriya Air Marshal Oladayo ya jaddada aniyar daukacin jami’an tsaro Najeriya na samar da kyakkyawan yanayin rayuwa ga daukacin ’yan kasa da kuma baki dake zaune a kasar.
Ya ce ba za su taba gajiyawa ba a kokarin da suke yi na yakar ’yan ta’adda a duk inda suke domin samar da yanayi mai kyau ga masu saka jari ’yan kasashen waje. (Garba Abdullahi Bagwai)