• English
  • Business News
Wednesday, August 13, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jakadan Sin Dake Najeriya Ya Gana Da Janar Gowon

by CMG Hausa
3 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Jakadan Sin Dake Najeriya Ya Gana Da Janar Gowon
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Labarai Masu Nasaba

PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

Jakadan kasar Sin a tarayyar Najeriya Cui Jianchun, ya gana da tsohon shugaban gwamnatin sojan kasar Yakubu Gowon, wanda ya taba ba da gagarumar gudummowa ga ci gaban huldar diplomasiyyar tsakanin kasashen biyu.

Jakada Cui ya bayyana cewa, a halin yanzu, huldar dake tsakanin Sin da Najeriya tana gudana yadda ya kamata karkashin kokarin da gwamnatoci da al’ummomin sassan biyu suke yi, kana kasashen biyu suna goyon bayan juna a fannin siyasa, kuma suna taimakawa juna wajen ci gaban tattalin arziki da cinikayya.

Ya ce a nan gaba, kasar Sin tana son hada hannu da Najeriya domin tabbatar da sakamakon da aka samu yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, tare kuma da ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba.
A nasa bangaren, janar Gowon ya bayyana cewa, “Kasar Sin da al’ummun Sinawa dake karkashin jagorancin JKS, sun samu babban sakamako wajen gina kasarsu, na taba ziyartar kasar Sin sau da dama a shekarun 1980 da na 1990, da idona na ga yadda kasar Sin ta sauya daga kasar aikin gona dake fama da koma baya, zuwa kasar masana’antu mai wadata.

Ya dace kasashe masu tasowa kamar Najeriya su koyi fasahohin gudanar da harkokin kasa irin na kasar Sin. Hakika a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, tarayyar Najeriya ita ma ta samu babban ci gaba a fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, mun godewa kasar Sin saboda goyon bayan da take ba ci gaban Najeriya a fannoni daban daban.” (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sabuwar Manufar Amurka Kan Sin Ba Ta Canja Tunaninta Na Yakin Cacar Baka Da Fin Karfi Ba

Next Post

Rundunar Sojin Sin Ta Kira Taro Kan Yanayin Tsaro A Gabar Tekun Guinea

Related

PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao
Daga Birnin Sin

PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao

49 minutes ago
Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
Daga Birnin Sin

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

19 hours ago
Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika
Daga Birnin Sin

Ilimin Fasahar Zamani Dama Ce Ta Samun Kyakkyawar Makoma A Afrika

20 hours ago
Sin Ta Ware Yuan Miliyan 170 Domin Ayyukan Tallafi Ga Sassan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Ware Yuan Miliyan 170 Domin Ayyukan Tallafi Ga Sassan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa

21 hours ago
Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa
Daga Birnin Sin

Xi: Sin Da Brazil Na Iya Zama Misalin Hadin Kai Da Dogaro Da Kai Ga Kasashe Masu Tasowa

22 hours ago
Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Cinikayya Ta Kasar Sin Ta Yi Karin Haske Kan Batun Saka Wasu Sassa Cikin Wadanda Ta Sanyawa Takunkumin Sayar Musu Da Kayayyaki

23 hours ago
Next Post
Rundunar Sojin Sin Ta Kira Taro Kan Yanayin Tsaro A Gabar Tekun Guinea

Rundunar Sojin Sin Ta Kira Taro Kan Yanayin Tsaro A Gabar Tekun Guinea

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati

August 13, 2025
PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao

PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao

August 13, 2025
NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano

NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano

August 13, 2025
Za Mu Nome Dazuka Don Magance Matsalar Tsaro A Neja – Bago

Gwamnatin Neja Ta Tabbatar Da Kama Hatsabibin Ɗan Bindiga, Abubakar Abba

August 13, 2025
ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

ADC Ta Dakatar Da Shugabanta Da Wasu Jiga-jigai 3 A Kebbi

August 13, 2025
An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe

August 13, 2025
PDP Ta Soki Gwamnatin Tinubu Kan Tsare Tambuwal Da EFCC Ta Yi

Tambuwal: ’Yan Nijeriya Sun Soki EFCC Kan Rashin Kama Okowa, Ganduje Da Yahaya Bello

August 13, 2025
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita

August 13, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi

August 12, 2025
Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

August 12, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.