A ranar 18 ga watan Yunin wannan shekara ce, cibiyar kula da baki da yawon bude ido ta Najeriya, ta shirya bikin “ranar dafa abinci mai dorewa ta kasa da kasa” a babban dakin taro dake Abuja, babban birnin Najeriya.
An gayyaci jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun don halartar bikin tare da gabatar da al’adun kasar Sin.
Jakada Cui ya bayyana cewa, yana fatan kasashen Sin da Najeriya, za su hada gwiwa don cimma moriyar juna a nan gaba. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp