A ranar Talatar da ta gabata, Jakadan kasar Sin a Amurka, Xie Feng ya jaddada cewa, kakaba haraji ko yakin ciniki ba za su iya magance matsaloli ba, ballantana kuma kawo cikas ga ci gaban kasar Sin.
Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 20 da kafuwar babbar kungiyar ‘yan kasuwar kasar Sin da ke Amurka (CGCC) da aka gudanar a birnin New York na kasar ta Amurka, Xie ya bayyana cewa, barazanar haraji ba za ta taba yin tasiri a kan Sinawa ba, a maimakon haka, masu yi za su buge ne da illata ginshikin yaki da miyagun kwayoyi da hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka, da kara tsadar kayayyaki ga iyalan Amurkawa da harkokin kasuwanci a kasar.
- Ranar Kafar Rediyo Ta Duniya: Minista Ya Buƙaci Gidajen Rediyo Su Faɗakar Da Jama’a Kan Sauyin Yanayi
- Amurka Ba Za Ta Cimma Burinta Bisa Matakin Kara Harajin Kwastam Kan Ma’adanan Karfe Da Goran Ruwa Ba
Jakadan ya nanata cewa, kasar Sin ita ce kasa ta farko a duniya da ta tsara abubuwan da ke da alaka da kwayoyin fentanyl a hukumance a karkashin mataki na bai-daya, tare da tsaurara matakan tsaro a kai, sakamakon tsare-tsaren jadawalin da aka yi na amfani da mafiya yawan abubuwan da suke da alaka da kwayoyin na fentanyl.
Ya kuma kara da cewa, sakamakon hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Amurka kan yaki da muggan kwayoyi a bayyane suke ta yadda kowa zai iya gani, kana ya yi gargadin cewa, kakaba karin haraji kan kasar Sin bisa hujjar batun fentanyl ba za ta haifar da da mai ido ba. (Abdulrazaq Yahuza Jere)