An bude taron shekara-shekara na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14 da safiyar jiya Talata a nan birnin Beijing. Jakadun kasa da kasa dake nan kasar Sin sun halarci taron budewar, inda suka bayyana cewa, kuzarin tattalin arzikin Sin na amfanar kasashen duniya, kuma ingantaccen ci gaba mai karko da Sin take samu, zai kawowa dukkanin fadin duniya zarafi mai yakini.
Jakadiyar Sao Tome da Principe madam Isabel Domingos, ta bayyana cewa, karuwar tattalin arzikin Sin a shekarar 2023 ya kai kashi 5.2%, matakin da ya mikawa duniya wani sako mai kyau. A ganinta, basirar Sin abin koyi ce ga sauran kasashe, kana ta yabawa yadda Sin take sauke nauyin dake wuyanta da cika alkawarinta.
A nasa bangare kuwa, mashawarci ga jakadan kasar Kamaru dake kasar Sin ya nuna cewa, tattalin arzikin Sin na da matukar alaka da na duniya, inda yake karfafa farfadowar tattalin arzikin duniya. Kaza lika, a bana, Sin ta tsai da shirin shimfida wasu hanyoyi, da gina madatsan ruwa da sauransu, bisa shirin “ziri daya da han hanya daya”, don taimakawa ci gaban Kamaru, wanda hakan zai kyautata zamantakewar jama’ar kasar. (Amina Xu)