Kwamishinan ‘yansandan Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba Bakori, ya roƙi al’umma da su riƙa kai rahoton duk wani ɗan sanda da ke karɓar cin hanci ko taimaka wa masu laifi.
Ya ce idan akwai ɗan sanda da ke haɗa baki da ɓata-gari ko dillalan ƙwaya, mutane su faɗa wa rundunar don a ɗauki mataki.
- Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Bayar Da Kiwon Lafiya Kyauta Ga ‘Yan Fansho Masu Karamin Karfi
Wannan bayani ya biyo bayan wani matashi da ya fitar da wani bidiyo a shafukan sada zumunta, inda ya zargi wasu ‘yansanda a unguwar Sheka da karɓar kuɗi daga hannun masu laifi, musamman masu sayar da ƙwaya.
Matashin ya ce wasu daga cikin ‘yansandan ma suna sanar da masu laifi kafin a zo a kama su, don su samu damar tserewa.
Ya ce saboda irin wannan halayya, ya zama da wuya a shawo kan matsalolin shaye-shaye da faɗan daba a Kano.
Kwamishinan ya ce tuni ya ba da umarni a fara bincike kan waɗanda ake zargin.
Ya kuma tabbatarwa da jama’a cewa duk wanda ya kawo ƙorafi za a saurare shi, ba tare da an tsananta masa ba.
A cewar rundunar, an daɗe ana samun ƙorafi cewa wasu ɓata-garin ‘yansanda suna karɓar kuɗi daga masu laifi domin su rufa musu asiri.
Amma wannan karon, hukumar za ta bi sahun ƙorafin domin ganin an yi gyara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp