Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire (JAMB) ta kaddamar da wani kwamitin musamman domin bincikar al’amuran amfani da fasaha wajen yin magudin jarabawa da aka gano a yayin jarabawar UTME ta 2025.
Yayin kaddamar da Kwamitin Musamman Mai Mambobi 23 Kan Laifukan Jarabawa a ranar Litinin a Abuja, Shugaban JAMB, Farfesa Ishak Oloyede, ya nuna damuwa kan kara kwarewar masu magudin jarabawa, inda ya bayyana cewa sakamakon dalibai 6,458 na nan karkashin bincike bisa zargin shiga cikin magudin zamani na fasaha.
- EFCC Na Neman Surukin Atiku Abubakar Ruwa A Jallo
- Sanata Wadada Ya Fice Daga Jam’iyyar SDP Bayan Ganawa Da Tinubu
“Wannan shekarar mun gamu da abubuwa masu ban mamaki da dama, kuma mun ji zai fi kyau idan muka fadada hanyoyinmu. Muna kuma da yakinin cewa Allah ya albarkaci wannan kasa da tarin albarkatu da za mu iya amfana da su,” in ji Oloyede.
Oloyede ya jaddada cewa akwai bukatar daukar gaggawar mataki domin kare ingancin jarabawa.
“Magudin jarabawa wani abu ne da dole mu yi yaki da shi da kowace digon jinin da ke jikimmu,” in ji shi, yana gargadin cewa idan ba a shawo kan wannan matsala ba, zai iya lalata fannoni da dama tare da bata sunan Nijeriya.
Oloyede ya bayyana cewa an tura al’amuran “na al’ada” guda 141 na magudin jarabawa zuwa ga kwamitin ladabtarwa na JAMB, yana mai kara da cewa wannan sabon kwamiti zai yi aiki da “laifuka na musamman,” irin su hada hotuna (image blending), kirkirar rashin kwayar halitta (albinism falsification), hada yatsu (finger pairing), da kuma kokarin karya tsarin sadarwar Local Area Network na wasu cibiyoyin CBT.
Ya jera ayyukan da aka dora wa kwamitin, wanda suka hada da binciken dukkan al’amuran hada hotuna (image blending), hada yatsu (finger blending), karya da’awar rashin kwayar halitta (albinism) da kuma kirkirar sakamako a jarabawar 2025.
Haka kuma, gano hanyoyi, dabaru, kayan aiki da fasahohin da aka yi amfani da su wajen aikata wadannan laifuka, nazarin manufofin jarabawa da na rajista na yanzu da kuma bayar da shawarwari kan inganta su.
Bugu da kari, an dora wa kwamitin alhakin tantance ko wadanda ake zargi dalibai 6,458, ban da wadanda ke cikin rukuni na albinism, suna da hannu ko a’a, saboda sakamakonsu na nan a dakace.
Kwamitin zai kuma “ba da shawarar hukunci ko ladabtarwa da suka dace ga duk wani mutum ko rukuni da aka samu da laifi.”
“Ku gabatar da tsari mai wayewa domin gano, dakile da kuma hana magudin jarabawa da fasaha ta zamani ke taimakawa a nan gaba.
“Kuma ku yi la’akari ku bayar da shawara kan duk wata matsala da ta shafi wadannan al’amura,” in ji shi.
Kwamitin na da makonni uku bayan kaddamarwa don gabatar da rahoton aikinsa.
“Mun zabi makonni uku ne saboda an ce adalci da aka jinkirta tamkar adalci da aka hana ne.
“A cikin kusan makonni hudu, za a rufe karbar dalibai. Kuma muna ganin wadanda ba a same su da laifi ba su sami damar su,” in ji Oloyede.
Shugaban Kwamitin, Dakta Jake Epele, ya yaba da jagorancin Oloyede tare da yin alkawarin cewa kwamitin zai yi aiki tukuru wajen cika wannan aiki.
Mambobin kwamitin sun hada da Farfesa Muhammad Bello, Farfesa Samuel Odewummi, Farfesa Chinedum Nwajiuba, Farfesa Tanko Ishaya, Farfesa Ibe Ifeakandu, Tsohon Kwamishinan ‘Yansanda Fatai Owoseni, Dakta Chuks Okpaka na Microsoft Africa, da Shugaban Kungiyar Daliban Nijeriya (NANS), tare da wasu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp