Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta musanta zargin cewa, majalisar dokoki ta Nijeriya na bincikenta kan kashe Naira biliyan 9 wajen ciyar da abinci da walwala da kuma tsaro.
Hukumar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Dr Fabian Benjamin ya fitar ta ce, hukumar a ranar Litinin 13 ga watan Janairu, 2025 ta gurfana gaban kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai da na majalisar wakilai kan harkokin kudi domin kare kudirinta na kasafin kudin 2025, bisa bin ka’idojin da doka ta tanada.
- Ana Hasashen Yawan Tafiye-Tafiye Za Su Kai Biliyan 9 Yayin Bikin Bazara Na Kasar Sin
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
“Yana da mahimmanci a lura cewa abin da JAMB ta gabatar a gaban kwamitin ba wai yadda ta kashe kasafin kudaden da aka ware mata ba ne na 2024, kudirin kasafin kudin 2025 ne kawai, don haka, wannan ikirarin kashe kudade ba su da tushe.” In ji shi
Ya ce a yayin zaman, ba a gabatar da wani abin da aka kashe a shekarar 2024 na Naira biliyan 1.1 don ciyarwa ko wani abu makamancin haka ba.