Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta amince da cewa, tangarda a na’urar rumbun tattara sakamakon jarabawar ne ya shafi sakamakon jarabawar da daliban suka rubuta ta shekarar 2025 (UTME).
Shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
- A Sa Hikima Da Dabara Yayin Da Ake “Wasan Kati ” Da Kasar Amurka
- Amurka Da Saudiyya Sun Ƙulla Yarjejeniyar Dala Biliyan 600 Kan Tsaro, Makamashi Da Fasaha
Sakamakon haka, hukumar ta sake sanya ranar da za a sake rubuta jarabawar ga dalibai 379,997 a Jihohi biyar na Kudu maso Gabas da Jihar Legas da lamarin ya shafa.
Oloyede, wanda ya bayyana tangardar a matsayin “zagon kasa” ga shirin jarabawar UTME ta 2025, ya ce, wadanda abin ya shafa za su fara samun sako a wayar salularsu daga Hukumar daga ranar Alhamis, 15 ga Mayu, 2025.
Daga cikin dalibai miliyan 1.9 da suka zana jarabawar UTME ta shekarar 2025, sama da miliyan 1.5 aka bayar da rahoton, sun samu maki kasa da 200 daga cikin mafi girman maki 400, lamarin da ya haifar da damuwa a bangaren ilimi na kasar.
UTME ta wannan shekara, ta gamu da koma baya sosai, wanda ya haifar da damuwa tsakanin ɗalibai, iyaye, da malamai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp