Jami’an kasashen Sin da Habasha sun yi kira da a kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, don kara kuzarin bunkasa kasashe masu tasowa, da karfafa zamanantarwa, tare da samar da ci gaba mai inganci a fadin Afirka.
An bayyana hakan ne a yayin wani taron kara wa juna sani mai taken “Sin a lokacin bazara: Samar da damammaki tare da tattaunawa ta duniya,” da aka gudanar ranar Talatar da ta gabata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. Ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Habasha da rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ne suka shirya taron.
- Tabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A SinTabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A Sin
- Yawan Bishiyoyin Da Aka Dasa A Kasan Kasar Sin Ya Kai Kashi 25%
Da yake jawabi a taron, jakadan kasar Sin dake Habasha, Chen Hai, ya bayyana cewa, kasar Sin a shirye take ta nuna wa saura irin gogewarta ta zamani don tallafa wa samar da ci gaba mai inganci a kasar Habasha da sauran kasashen Afirka.
Jakadan ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da huldar diflomasiyya da Afirka da ma sauran kasashen duniya bisa ka’idojin makoma ta bai-daya, da samun bunkasa cikin lumana, da nuna adawa da mulkin malaka’u, tare da nuna goyon baya ga samun daidaiton kasa da kasa.
A nasa bangaren, karamin ministan tsare-tsare da raya kasa na kasar Habasha, Bereket Fesehatsion ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Habasha da kasar Sin yana nuna kyakkyawan misali ga hadin gwiwar kasashe masu tasowa, inda kasar Sin ke taka muhimmiyar rawa wajen habaka sauye-sauyen tattalin arzikin Habasha, ta hanyar bayar da lamuni da tallafi na dogon zango domin raya ababen more rayuwa. (Mai Fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp