Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a ƙaramar hukumar Funtua, Jihar Katsina, sun mayar da kuɗi Naira miliyan 6.2 da sauran kayayyaki da suka samu a wajen wani hatsarin mota da ya auku.
Hatsarin ya auku a ƙauyen Dikke, a kan titin Gusau zuwa Sakkwato, inda mutane biyu suka rasa rayukansu, yayin da wasu 16 suka jikkata bayan birki ya ƙwace wa diraben motar.
- Kafafen Sada Zumunta Na Zamani Suna Taimakawa Wajen Ta’azzara Matsalar Tsaro A Arewa – Yari
- Kotu Ta Ɗaure Mai Horas Da ‘Yan Wasa Shekaru 8 Sakamakon Zargin Luwaɗi Da Ƙaramin Yaro A Kano
Jami’an FRSC sun isa wajen cikin gaggawa, inda suka ceto waɗanda suka ji rauni suka kuma kai su Asibitin Sarkin Maska da ke Funtua domin jinya.
Muƙaddashin kwamandan hukumar a jihar, Ali Murtala, ya ce jami’ansa sun gano Naira miliyan 6.2 da wayoyi huɗu wanɗanda darajarsh ta kai Naira 550,000, kuma sun mayar da su ga masu su.
Ya yaba da gaskiya da ƙwazon jami’ansa wajen gudanar da aikin ceto.
Wani daga cikin waɗanda suka ji rauni, wanda shi ne mai kuɗin, ya gode wa jami’an FRSC bisa gaskiya da amana da suka nuna, yana mai cewa abin koyi ne ga kowa.
FRSC ta gargaɗi direbobi da su riƙa kula da motoccinsu akai-akai tare da bin ƙa’idojin hanya domin guje wa aukuwar haɗura.