Hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta cafke manyan motoci 15 dauke da kayan abinci a jihar Sokoto a kokarinta na hana fasa kwauri wanda ya ta’azzara tsadar kayayyaki a Nijeriya.
Abubakar Chafe, mai magana da yawun hukumar Kwastom, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Asabar cewa an kama motocin a kan hanyar Gwadabawa-Illela.
- Gwamnonin PDP Sun Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Tsadar Rayuwa
- Ƙungiyar Ƙwadago Za Ta Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Adawa Da Tsadar Rayuwa
Chafe ya ce an yi kama motocin ne saboda yawan abincin da suke dauke da shi.
Ya ce a halin yanzu manyan motocin na hannun hukumar kuma an fara gudanar da bincike don gano masu kayan da inda za a kai kayan abincin.
Ya bayyana cewa rundunar hadin guiwa ta kwastom reshen Sokoto da jami’an sashin lura da ayyuka na tarayya da kuma sashin leken asiri na hukumar ne suka gudanar da aikin.
Chafe ya kara da cewa aikin ya zama dole duba da irin hauhawar farashin da kayan abinci ke yi a kasar.