Jami’an Hukumar Kwastam ta Nijeriya, masu aiki a yankin Sokoto/Zamfara sun ƙi amincewa da cin hancin Naira miliyan ₦1.5m da wasu da ake zargin ɓarayin ƙarfen jirgin ƙasa ne suka bayar a Kajiji da ke kan titin Kebbi a Jihar Sakkwato.
An bayar da cin hancin ne a ranar Asabar ɗin da ta gabata lokacin da jami’an tsaro suka tare wata babbar mota dauke da kwantena mai tsawon kafa 20 cike da ƙarafunan titin jirgin ƙasa, lamarin da ya sa aka kama mutanen uku da ake zargi.
- Gwamnati Za Ta Samar Da Tsaro A Filayen Hakar Ma’adanai —Alake
- ‘Yansanda Sun Karyata Jita-jitar Kai Harin Garkuwa Da Mutane A Jami’ar BUK
Kwanturolan hukumar, Kamal Muhammed, ne ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin, inda ya ce waɗanda ake zargin sun gaza bayar da shaidar izini daga ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ta nuna an amince su kwashi kayan, kuma sun yi yunƙurin ba wa jami’an cin hancin Naira miliyan 1.5, tare da bayar da ₦300,000 a nan take. Jami’an sun zaɓi tsare waɗanda ake zargin ne saboda kishin ƙasa da kuma mutunci.
An miƙa waɗanda ake zargin, da babbar motarsu, da kayan da ke cikinta, da tsabar kuɗin ₦300,000 ga hukumar NSCDC ta Sokoto domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.