Mahukunta Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) da rundunar ‘yansandan jihar Kano sun karyata jita-jitar da aka yada cewa, masu garkuwa da mutane sun kai hari Jami’ar. Sun bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar mara tushe.
Mataimakin magatakarda kuma jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Lamara Garba, a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata, ya ce, ba a taba samun matsalar sace-sacen jama’a a cikin harabar jami’ar ba, yana mai cewa, tuni jami’ar ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron lafiyar jama’ar jami’ar.
- Gwamnatin Tarayya Ta shirya Kaddamar Da Shirin Baiwa Dalibai Bashi
- Gwamnatin Filato Ta Sanya Dokar Hana Fita A Karamar Hukumar Mangu
Sanarwar ta bayyana cewa, “Mahukuntan Jami’ar Bayero ta Kano sun samu sanarwar karya game da cewa, an samu tabarbarewar tsaro a jami’ar.
“Muna so mu bayyana cewa, ba a taba samun matsalar yin garkuwa da mutane ba a cikin harabar jami’ar ba, jami’ar ta dade da daukar duk matakan da suka dace don tabbatar da amincin ma’aikata da ɗaliban jami’ar.
“Mun kadu matuka kan yadda wasu marasa kishin kasa ke kirkirar labaran karya, kuma duk da sanin cewa, hakan zai haifar da firgici ba wai a cikin jami’ar kadai ba har ma a cikin al’ummomin jihar da ma sauran wurare.”
Rundunar ‘yansandan Kano ta bayyana a shafinta na X (Twitter), @KanoPoliceNG cewa, a rahoton da jami’anta da ke jami’ar suka bayar ya tabbatar da labarin karya ne.