Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun yi artabu da miyagu wadanda suka zagaye su tare da dakile dukkan hanyoyin fita a kauyen Opuje da ke Karamar Hukumar Owan ta Yamma a Jihar Edo yayin da jami’an suka kai sumame kan gidajen ajiya da aka cika makil da tan-tan na miyagun kwayoyi.
Miyagun bayan bude wuta, sun raunata mutane uku, inda daya daga ciki harsashi ta same shi a kwakwalwa.
- Iwobi Ya Jefa Kwallo 2 Yayin Da Fulham Ta Lallasa Forest Da Ci 5-0
- Kotu Ta Yi Wa Dan Fashi Daurin Rai Da Rai A Zamfara
Wannan yana zuwa ne watanni 11 bayan da gungun matasa dauke da muggan makamai da ke yi wa masu safarar miyagun kwayoyi aiki suka far wa jami’an hukumar da suka kawo sumame kauyen don lalata tantunan ajiya wadanda aka boye sama da kiligiram 317,417 na wiwi.
Zuwa yanzu dai an samu kama mutane uku: Omoruan Theophilus mai shekaru 37; Aigberuan Jacob mai shekaru 42 da kuma Ekeinde Anthony Zaza mai shekaru 53.
Kauyen na Opuje yayi kaurin suna wajen noman ganyen wiwi, inda masu safarar miyagun kwayoyi suka dade suna zuba hannun jari a ciki tare da lalata bishiyoyi don samun manyan gonakin wiwi na kadadodi daruruwa.
Bayan girbe haramtaccen ganyen, sukan gina manyan gidajen ajiya a cikin dajin sannan su dauki matasa su ba su muggan makamai don tsaron gidan ba kakkautawa.
Biyo bayan bayanan sirri cewa masu safarar miyagun kwayoyin sun cika gidajen ajiyan su a dajin saboda dillanci a bukukuwan karshen shekara, hukumar NDLEA ta shirya zaratan jami’ai saboda kai sumame dajin don dakile dillancin da kuma lalata gidajen ajiyan miyagun kwayoyin.
A yayin hakan ne aka lalata gidan ajiya da ke dauke da kilogiram 6,000 na wiwi a Ujiogba dake Karamar Hukumar Esan ta yamma a makon da ta gabata.
To amma a yayin wannan aikin, zaratan jami’an na hukumar sun tsinci kansu cikin matsanancin musayar wuta da miyagu a safiyar Litinin 4 ga watan Disamba a yayin da suka nufi dajin Opuje inda suka dakile dukkan hanyoyi don hana jami’an NDLEA fita.
Amma jami’an bayan sun dauki awanni biyu suna ba ta kashi, sun samu nasarar fita daga dajin.
Sai dai kafin jami’an su fita, ‘yan bindigan sun raunata jami’ai uku, inda daya daga ciki harasashi ta same shi har cikin kwakwalwa, inda motocin jami’an suka samu illa matuka daga harasasai.
Jami’an da suka samu raunin an garzaya da su nan take zuwa asibiti, inda shi kuma wanda ya samu rauni a kwakwalwa aka yi masa tiyata aka cire harsashin daga cikin kwakwalwarsa a jiya Laraba 6 ga watan Satumba.
A yayin da yake martani dangane da harin da aka kai wa jami’an, shugaban hukumar NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya yi gargadin cewa wadanda suke daukar nauyin kai hari kan jami’ai a bakin aiki ba za su taba samun aminci ba, kuma komai dadewa za su girbi abin da suka shuka kamar yanda doka ta tanadar.
Kazalika, Marwa ya jinjina wa jami’an da suka kai sumamen, inda ya ce ko kadan, hare-haren miyagu ba zai sa kasa a guiwar hukumar ko ya hana ta dakile dillalan miyagun kwayoyi daga lalata al’umma a kasar nan ba.