Jami’an tsaro na yin ganawar sirri da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Sarki Sanusi II a fadar Sarkin Kano.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo jihar da zummar komawa kan kujerar masarautar Kano.
- Matsalolin Gidan Aure (3) Daure Fuska Da Rashin Nuna Damuwa Da Mace
- DSS, Sojoji Da Duk Jami’an Tsaro Sun Hallara a Fadar Aminu Ado
Hakan ya haifar da tashe-tashen hankula, lamarin da ya sanya aka jibge jami’an tsaro a fadin jihar.
Aminu Ado Bayero ya sauka a Kano a misalin karfe na safe, bayan da majalisar dokokin jihar ta rushe sauran masarautun da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro, inda ya sauka a karamar fadar Nassarawa.
Idan ba a manta ba a ranar Juma’a ne majalisar dokokin jihar ta rushe sarakunan tare da dawo da Sarkin Muhammadu Sanusi II.
Yanzu haka dai jami’an na gana wa da gwamnan da kuma sabon Sarkin domin nemo mafita da zaman lafiya a jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp