Rundunar ‘yan sandan jihar Yobe mai kula da albarkatun man fetur (YTPP) ta kai ziyarar bazata zuwa gidajen mai saboda karancin man fetur da ake fama dashi a jihar musamman a Damaturu babban birnin jihar.
A safiyar Larabar da ta gabata ne aka siyar da galan na man fetur PMS a kan kudi Naira N3,600 a fadin Damaturu a kasuwar bunburutu, lamarin da ya tilastawa masu motocin kasuwa da masu tuka keke napep karin kudin motar ga kowane fasinja.
Shugaban kwamitin jami’an wanda kuma shine babban sakatare na ma’aikatar kasuwanci da masana’antu Dakta Musa Abba Kolere, a lokacin da yake jawabi ga manema labarai, ya ce samamen ya zama dole domin wasu gidajen mai na da dabi’ar boye man fetur don son zuciyarsu da cutar da masu ababen hawa.
Kolere ya ce duk da cewa ba za su iya tilastawa gidajen man kara farashin litar man ba, amma yace, gwamnati ba za ta nade hannunta tana kallon gidajen man na haifar da wahalhalun da bai kamata ba ga jama’a.