Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kubutar da mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a hanyar Birnin Gwari-Gayam a wani sintiri da suke yi a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun na jihar Kaduna.
Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da harkokin cikin gida Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa sojojin sun yi batakashi da ‘yan bindigan a lokacin da suke sintiri a hanyar Birnin Gwari-Gyam-Kuriga-Manini na jihar.
Aruwan ya ce sojojin sun fatattaki ‘yan bindigar, inda suka tsere zuwa cikin dazuzzuka suka bar wadanda suka yi garkuwa da su din.
Sanarwar ta ce: “Sojojin sun ceto mutane bakwai da aka sace, wadanda aka bayyana sunayensu kamar haka: Joseph Ishaku, John Bulus, Gloria Shedrack (da ‘ya’yanta hudu): Jimre Shedrack, Jonathan Shedrack, Angelina Shedrack, Abigail Shedrack.”
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta yabawa sojojin tare da gode musu bisa jajircewar da suka yi wajen ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Aruwan ya kara da cewa, mutanen bakwai da abin ya shafa sun koma duk wurin iyalansu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp