Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kaduna ta kwato wayoyi 45 daga hannun wata kungiyar barayin da ke fashi da makami.
Haka kuma, Rundunar ta sanar da kama mutane shida bisa zargin fashi da makami, mutane biyar da ake zargin masu karbar kaya sata ne, da kuma wasu uku bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
- Nazari Kan Yadda Za A Iya Samun Wadatacciyar Riba A Kiwon Jimina
- Fim Na Nezha 2 Na Kasar Sin Ya Kara Samun Lambar Yabo
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, a cikin wata sanarwa ya ce, dakarun Operation Fushin Kada Tracking and Response Team ne suka gudanar da wannan kamen tsakanin 10 zuwa 18 ga Satumba.
A cewarsa, a ranar 11 ga Satumba, dakarun bisa sahihan bayanan sirri suka kama wani shahararren shugaban ‘yan daba, Fahad Babangida, tare da abokan aikinsa, Ahmed Lawal da Salahudeen Ibrahim.
Ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a lokacin da suke shirin kai hari kan wani tsohon ma’aikacin NNPC.
Bincike ya kuma kai ga cafke wani bangare na kungiyar karkashin jagorancin Babangida, wadanda aka gano sun hada da Isah Musa da Usman Abdullahi, wadanda suka amsa laifin karya shaguna da kuma yin fashi a yankin Rigasa.
Lokacin bincike, wadanda ake zargin sun ambaci masu karbar kayan sata da suka taimaka musu wajen sayar da su. Wannan ya kai ga cafke Kabiru Sabitu, wanda aka fi sani da Baban Godiya, Abdullahi Shehu da Yusuf Saleh.
Haka kuma, a ranar 10 ga Satumba, an kama wani mai suna Bello bisa zargin satar waya. Kamen nasa ya kai ga kwato wayoyi hannu 45 da kwamfutar tafi-da-gidanka, tare da kama masu karbar kayan sata nasa.
A wani nasara daban, a ranar 15 ga Satumba, tawagar sintiri daga sashen ‘yansanda na Kabala West ta tare wasu, Hassan (mai shekaru 19) da Abubakar (mai shekaru 21), a Unguwar Mu’azu Bypass. An kwato babur baki kirar TBS da bindigar 9mm pistol tare da harsasai uku daga hannunsu.
Haka kuma, a ranar 18 ga Satumba, jami’ai sun cafke Simon Haruna daga Karamar Hukumar Barikin Ladi, Jihar Filato, a Lambar Zango, Birnin Yaro, cikin Karamar Hukumar Igabi. Ana zargin yana tattaunawa kan sayar da bindigar Beretta pistol kafin a kama shi.
Tawagar ta kwato bindigar Beretta da aka kera a Amurka tare da harsasai uku daga hannunsa.
Kwamishinan ‘Yansanda, CP Rabiu Muhammad, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin bisa kwarewa, tare da tabbatar wa da mazauna jihar cewa rundunar ta himmatu wajen kawar da miyagun ‘yan ta’adda daga Jihar Kaduna.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da fadakarwa, tare da bayar da muhimman bayanai ga ‘yansanda a kokarin hadin gwiwa na tabbatar da tsaron jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp