Hukumomi a Birtaniya sun tsare dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP, Peter Obi kan zargin aikata wasu laifuka.
An ce an tsare Obi na tsawon sa’o’i, kuma jami’an tsaro sun yi masa tambayoyi, bayan da ya sauka a filin jirgin sama na Heathrow da safiyar Juma’a.
- Yawan Marasa Aiki A Nijeriya Zai Karu Zuwa kashi 41 A 2023
- NEMA Ta Karbi ‘Yan Nijeriya 152 Da Suka Dawo Daga Libya
Farfesa Chinyere Okunna, mataimakin shugaban Jami’ar Paul Awka, wanda kuma aminin Obi ne ya bayyana hakan a safiyar Laraba.
Okunna, wanda ya yi aiki tare da Obi a matsayin kwamishinan yada labarai, kwamishinan tsare-tsare da tattalin arziki, ya ce Obi wanda ya yi rayuwa cikin mutunci a Birtaniya wanda abun mamaki ne a ce an kama shi.
Ya ce alamu na nuna ana so a shafa masa kashin kaji ne tun da ya nuna ya ki aminta da sakamakon zaben 2023 na shugaban kasa da aka gudanar a watan Fabarairu.
Idan za a tunawa wani sautin muryar Obi ya fita inda aka jiyo shi yana rokar wani Fasto kan ya taimaka masa ya ci zaben 2023.
Sai dai Gwamnatin Tarayya ta soki Obi kan kalaman da ya yi a sautin da aka nada na wayar da ya yi da Faston din, inda gwamnati ta ce wannan cin amanar kasa ne.