Kamfanin ba da shawara kan haraji na duniya, (KPMG), ya yi hasashen cewa rashin aikin yi a Nijeriya zai karu zuwa kashi 40.6 idan aka kwatanta shi da na 2022 na 37.7.
KPMG ta yi cikakken bayanin wannan hasashen a cikin rahotonta na Hasashen Harkokin Tattalin Arziki na Duniya – H1 2023 a ranar Talata, inda ta bayyana cewa “ana sa ran rashin aikin yi zai ci gaba da zama babban kalubale a 2023 saboda karancin jarin da kamfanoni masu zaman kansu ke yi.
- Shugaban Bankin Duniya: Sin Da Indiya Sun Tsallake Koma Bayan Da Tattalin Arzikin Duniya Zai Fuskanta A Bana
- Mataimakin Firaminista:Sin Za Ta Ci Gaba Da Bunkasa Samar Da Kayayyaki Masu Inganci
Kazalika ta ce karancin masana’antu, da sannu a hankali zai kara tabarbarewa tattalin arziki”.
Rahoton ya kuma bayyana a wani bangare cewa ana sa ran kudin shiga zai ci gaba da habaka a sannu a hankali da kashi 3 a 2023 sakamakon koma bayan harkokin tattalin arziki da ke nuna lokutan sauyin siyasa a Nijeriya.
Haka kuma, ana sa ran za a samu koma bayan tattalin arzikin duniya a 2023 da kuma tasirinsa na ciniki da hada-hadar kudi.
“Bugu da kari, ci gaban zai haifar da mummunan tasiri ga manufar sake fasalin Naira da aka gabatar a karshen 2022 da farkon 2023 da kuma abubuwan da ke haifar da mjhimman sassan da ba na mai ba kamar masana’antu, kasuwanci, wurin kwana da abinci, sufuri, da sauran ayyuka, yana kara raguwar kudin shiga gaba daya a 2023,” in ji rahoton.
Dangane da sake farfadowar manyan al’amuran tattalin arziki, ta yi hasashen cewa, ana sa ran za a farfado da harkokin sadarwa, da harkokin kasuwanci, da kuma bangaren mai, saboda matakan da ake dauka na tunkarar matsalar tsaro.