Jami’an tsaro a filin wasa na Moshood Abiola National Stadium da ke Abuja sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga da Ƴan Jarida a rana ta uku na zanga-zanga kan yunwa da ƙuncin rayuwa.
Zanga-zangar, wadda ta fara cikin lumana, ta canza yanayi a ranar Asabar yayin da Ƴansanda suka harba hayaƙi mai sa hawaye da harsasai cikin iska, suna tarwatsa masu zanga-zangar da suka fara sake taruwa.
- Sin Ta Fadada Manufar Yada Zango A Kasar Ba Tare Da Biza Ba Zuwa Karin Tashoshi
- Rana Ta 3: Duk Da Dokar Hana Fita Masu Zanga-zanga Sun Fito A Kano
Jami’ai masu rufe fuska daga hukumar tsaro ta DSS sun iso wurin kuma nan take suka shiga cikin martani, wanda ya haifar da kamawa da kuma jikkatar mutane da dama.
Wannan ruguntsumin ya rutsa har zuwa ga Ƴan Jarida, inda harsasai suka samu motar da ke ɗauke da su yayin da suke ƙoƙarin barin wurin. Cibiyar kula da Ƴan Jarida ta Duniya (IPC) ta yi Allah wadai da waɗannan hare-hare, tana nuna damuwa kan yawaitar cin zarafi, da duka da hana Ƴan Jarida damar yin aikinsu a jihohi daban-daban.
Ƴan Jarida a Lagos, da Kano, da Abuja, da Calabar, da jihar Delta sun ruwaito cewa an ci zarafinsu, an ji musu rauni, kuma an lalata kayayyakin su daga hannun Ƴansanda da Ƴan daba.
Melody Akinjiyan, jami’ar kare ƴancin Ƴan Jarida ta IPC, ta soki waɗannan ayyuka, tana bayyana su a matsayin “wani abin alhini da ke maimaituwa a tarihi” kuma ta jaddada muhimmancin ƴancin Ƴan Jarida na rawaito al’amuran al’umma. Ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki waɗannan hare-hare kuma su tabbatar da adalci ga Ƴan Jaridar da aka cutar.