Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria, ta ƙaryata wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa jami’ar na da hannu wajen wani shiri na sirri kan haɗa makamin nukiliya a Nijeriya.
A wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a na jami’ar, Malam Auwalu Umar, ya fitar a ranar Asabar, jami’ar ta bayyana cewa wannan faifan bidiyon da aka samar ta hanyar na’urar ƙirƙirar bidiyo (AI-generated), ƙarya ne kuma an shirya shi ne don rikita jama’a da ɓata haƙiƙanin manufar ƙasar wajen amfani da makamashin nukiliya na lumana.
- Gombe Ta Ƙulla Yarjejeniya Da Rano Air Don Fara Jigila Tsakanin Abuja Zuwa Gombe
- Tinubu Ya Naɗa Shugabannin Jami’o’in Ilimi Na Tarayya Da Ke Zariya Da Kano
Umar ya bayyana cewa faifan bidiyon ya yi zargin cewa masana makamin a Nijeriya a shekarun 1980 sun yi ƙoƙarin samar da uranium mai ƙarfin makami a Kaduna, kuma masu bincike na ABU sun samo na’urorin centrifuge daga ƙasar Pakistan ta hanyar AQ Khan, abin da jami’ar ta ce babu wata hujja ko shaidar gaskiya a kai.
Ya ƙara da cewa a shekarar 1987, ABU tana da na’urar 14 MeV Neutron Generator kawai, wadda ta fara aiki a 1988. Jami’ar kuma ta bayyana cewa nuclear reactor ɗin farko a Nijeriya (NIRR-1) an kafa shi ne a 1996 tare da sa ido da hana yaɗuwar makaman nukiliya (IAEA), kuma aka ƙaddamar da shi a hukumance a 2004 domin bincike da aikace-aikacen zama na lafiya.
Umar ya jaddada cewa dukkan aiyukan nukiliyar Nijeriya ana gudanar da su ne bisa tsarin lumana da kuma bin ƙa’idodin ƙasa da ƙasa kamar yarjejeniyar NPT da Pelindaba Treaty, wadda ta haramta samar da makaman nukiliya.
Ya ƙara da cewa cibiyar Centre for Energy Research and Training (CERT) ta jami’ar ABU, wadda aka kafa tun 1976, tana aiki tare da IAEA da kuma ƙasashe kamar Amurka, da Rasha da China, kuma ba ta taɓa gudanar da wani shiri na makamin nukiliya ba.
A cewarsa, “ABU tana ci gaba da sadaukar da kai wajen inganta kimiyya da fasaha don ci gaban ƙasa da kuma tabbatar da zaman lafiya ta hanyar amfani da makamashin nukiliya ta hanya mai amfani da jama’a.”












