Jami’ar Ambrose Alli (AAU), Ekpoma ta lashe lambar yabon fasaha ta Nijeriya a fannoni uku.
Fannonin sun hada da gwarzon jami’ar jiha da ta lashe kambun shekara kan yanar gizonta, kwazo a bangaren bunkasa fasaha a jami’ar jiha da kuma kwazo a bangaren amfani da kafafen sadarwar zamani.
An mika lambar yabon ne a yayin babban taron Nigeria Technology (NITA) karo na 9, wanda ya gudana a karshen mako a jihar Legas.
- Adadin Kudin Shiga Na Yawon Bude Ido Na Cikin Gida Na Kasar Sin Ya Karu Da 114% A Watanni 9 Na Farkon Bana
- Sanatoci Sun Nemi A Rufe Hukumar AMCON Bayan Bacewar Naira Biliyan N146 Cikin Shekara Daya
Da ya ke amsar lambobin yabon a madadin jami’ar, mai rikon mukamin mukaddashin shugaba Farfesa Asomwan Sonnie Adagbonyin, wanda ya samu wakilcin Misis Abiola Laseinde, ya ce, wannan karramawar lalla za ta kara musu kumaji a wadanna fannoni.
Ya gode wa bangaren da su karramasu, ya sha alwashin cewa hakan zai kara basu damar su bunkasa dukkanin harkokin da suka shafi fasaha.
A jawabinsa na maraba, wanda ya jagoranci shirya bikin lambar yabon kuma babban jami’in gudanarwa na NITA, ya ce, an bayar da lambar ne domin nuna yabo kan hukumar da ta taka rawa a bangaren fasaha.